logo

HAUSA

Fannin Sadarwar Kasar Sin Ya Samu Bunkasar Kudaden Shiga

2021-12-26 19:29:58 CMG

Fannin Sadarwar Kasar Sin Ya Samu Bunkasar Kudaden Shiga_fororder_telecom

Alkaluman da hukumomi suka fidda ya nuna cewa, kamfanonin sadarwar kasar Sin sun samu gagarumar bunkasar kudaden shiga a watanni 11 na farkon shekarar da muke ciki.

Jimillar kudaden shigar kamfanonin ya karu da kashi 8.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wanda ya zarce yuan RMB triliyan 1.35 (kwatankwacin dala biliyan 212) tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin ta bayyana.

Alkaluman sun nuna cewa, adadin ya ragu da kasa da digo daya daga adadin watan Janairu zuwa Oktoba.

A cewar ma’aikatar, ya zuwa karshen watan Nuwamba, manyan kamfanonin sadarwar guda uku na kasar Sin, da suka hada da China Telecom, China Mobile da China Unicom, suna da masu amfani a wayoyin hannu sama da mutane biliyan 1.64, adadin da ya karu da mutane miliyan 47.92 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. Adadin masu amfani da wayoyin hannu na fasahar 5G ya kai miliyan 497, inda ya karu da mutane miliyan 298 daga karshen shekarar bara.

Manyan kamfanonin sadarwar uku sun kuma samu karuwar adadin masu amfani da fasahar intanet mai saurin gaske ya zuwa karshen watan Nuwamba, inda adadin ya karu da mutane miliyan 51.85 daga karshen shekarar bara wanda adadinsu ya kai miliyan 535.(Ahmad)

Ahmad