logo

HAUSA

Masana: Ya dace a hada kai domin dakile sabon kalubalen yaki da ta’addanci a Afirka

2021-12-26 16:55:51 CRI

Kwanakin baya an shirya taron karawa juna sani kan yaki da ta’addanci na kasa da kasa karo na biyu a zahiri da kuma ta kafar bidiyo, jami’an gwamnatocin kasashe 16, da masu kula da hukumomin nazarin harkokin dake shafar yaki da ta’addanci, da masanan da abin ya shafa, sun halarci taron, inda suka bayyana cewa, a halin yanzu matsalolin talauci da sauran rikice-rikicen zamantakewar al’umma suna kara tsanani sakamakon yaduwar cutar COVID-19, haka kuma ayyukan ta’addancin da kasashen Afirka suke fuskantar suna cigaba da karuwa, don haka ya dace bangarori daban daban su hada kai su dauki matakai tare domin dakile sabon kalubalen yaki da ta’addanci a nahiyar Afirka.

Mukadashin darektan cibiyar nazarin yaki da ta’addanci ta kungiyar tarayyar Afirka AU ya bayyana yayin taron cewa, yanzu kalubalen ta’addanci yana bazuwa cikin sauri mai matukar ban tsoro a nahiyar Afirka, musamman ma bayan yaduwar cutar COVID-19.

Jami’in yaki da ta’addanci na kasar Sin Gao Fei, ya yi tsokaci cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasashen Afirka sun fi fama da ayyukan ta’addanci, shi ya sa yana ganin cewa, ya dace a kafa tsarin kasa da kasa mai adalci bisa ka’idojin MDD, ta yadda za a kawar da ta’addanci daga tushe, tare kuma da daidaita matsalolin ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa.(Jamila)