logo

HAUSA

Mali ta musanta tura sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha a yankunanta

2021-12-26 19:32:13 CMG

Mali ta musanta tura sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha a yankunanta_fororder_mali

Kasar Mali ta musanta tura sojojin haya na kamfanin Wagner mai zaman kansa na kasar Rasha zuwa yankunan kasar.

A wata sanarwar da aka fitar da yammacin ranar Juma’a, gwamnatin kasar Mali ta kuma bukaci a gabatar mata da hujjoji daga majiyar mai zaman kanta da ta yada wannan zarge-zarge.

Hukumomin kasar Mali sun fayyace cewa, akwai jami’an bada horo na kasar Rasha a kasar ta Mali wadanda ke aikin karfafa rundunar tabbatar da tsaron kasa ta SDF, inda ta bayyana cewa, ya kamata a yanke hanzari kan gwamnatin Mali bisa dogaro da hujjoji ba ta hanyar yada jita-jita ba, kana gwamnatin kasar ta jaddada cewa, abinda ke tsakaninta ta Rasha shine hulda ce ta kasa da kasa.

Wasu abokan huldar kasar Mali na kasa da kasa goma sha biyar na yammacin duniya ne suka fidda sanarwar hadin gwiwa a ranar Alhamis, inda suka yi Allah wadai da zuwa tawagar dakarun tsaro na Wagner zuwa kasar Mali. Sun bayyana cewa, babu abinda dakarun sojojin kamfanin  Wagner zasu haifar face sake lalata al’amurran tsaron kasar ta Mali, inda suka bukaci gwamnatin rikon kwaryar kasar Malin cewa, maimakon daukar wannan mataki kamata yayi tayi kokarin farfado da dokokin tsarin mulkin kasar ta hanyar shirya zabuka a kasar.(Ahmad)

Ahmad