logo

HAUSA

Kakakin gwamnatin Xinjiang: Ba a fuskantar “aikin tilas” a jihar bisa yarjejeniyar kasa da kasa

2021-12-26 16:55:05 CRI

Kakakin gwamnatin Xinjiang: Ba a fuskantar “aikin tilas” a jihar bisa yarjejeniyar kasa da kasa_fororder_新疆-4

Yau Lahadi 26 ga wata, kakakin ma’aikatar watsa labarai na gwamnatin jama’ar jihar Xinjiang ta kasar Sin, Yilijiang Anayiti, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, al’ummun jihar ‘yan kabilu daban daban suna zaben ayyukan da suke yi kamar yadda suke so, kuma ana kare hakki da moriyar ma’aikatan jihar ne bisa tsarin dokar kundin mulkin kasar Sin, da dokar ‘yan kwadago, da dokar kwangilar aiki, da dokar manyan laifuffuka, da dokar kiyaye kwanciyar hankali, da dokar sa kaimi kan samar da aiki, da dokar inshura kan zamantakewar al’umma da dai sauransu dokoki.

Kakakin ya kara da cewa, ko daga ma’anar yarjejeniyar kasa da kasa, ko daga tanadin dokokin kasar Sin, ko kuma daga hakikanin yanayin da jihar Xinjiang ke ciki, babu alama da ake ganin ana fuskantar “aikin tilas” a jihar Xinjiang.(Jamila)