logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Sakamakon Koyon Tarihin Jam’iyyar JKS

2021-12-25 16:26:16 CRI

Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Sakamakon Koyon Tarihin Jam’iyyar JKS_fororder_xjp

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC, ya yi kira da a inganta sakamakon da aka samu cikin gangamin nazari da koyon tarihin jam’iyyar.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsakiya na hukumar sojojin kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a baya bayan nan.

An gudanar da wani taro a ranar Juma’a a birnin Beijing, domin nazari kan gangamin,wanda aka gudanar da shi tsakanin dukkan ‘yan jam’iyyar a shekarar 2021, wadda kuma ita ce shekarar da aka cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar.

A matsayin wani muhimmin mataki da kwamitin tsakiyar CPC ya dauka, gangamin ya ilmintar da dukkan ‘yan jam’iyyar, da jami’an jam’iyyar daga sassa daban daban ta fuskar siyasa da ruhi.

Ta hanyar gangamin, jam’iyyar ta kara samun ingantuwar tunani kan tarihinta da kuma samun kwarin gwiwa, kana ta kyautata kwarewarta a fannonin yin kirkire-kirkire, hadin kai da yin gwagwarmaya. (Ahmad)

Ahmad