logo

HAUSA

Taron kolin demokuradiyyar da Amurka ta gudanar yana da yunkurin siyasa cikin sirri

2021-12-25 17:11:39 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a taron manema labarun da aka gudanar a jiya cewa, kasar Amurka ta samar da wani dandali ga Luo Guancong, wani mai neman ‘yancin kan yankin Hong Kong, wanda ya shaida cewa, taron kolin demokuradiyya da Amurka ta gudanar yunkuri ne na siyasa cikin sirri.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, an gabatar da takaitaccen bayanin taron kolin demokuradiyyar a shafin internet na majalisar harkokin wajen kasar Amurka, inda aka gabatar da ra’ayin da mai neman ‘yancin kan yankin Hong Kong Luo Guancong ya bayyana a taron kolin.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, harkokin yankin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kowace gwamnati ko hukuma ko kuma wasu mutunen kasashen waje ba su da iznin tsoma baki a harkokin yankin, yunkurin da ake yi ta hanyar fakewa da batun yankin Hong Kong don kawo illa ga ikon mulkin kan kasar Sin da tsaronta da moriyar samun bunkasuwarta ba zai cimma nasara ba. Babu shakka za a nuna kin amincewa da masu tada zaune tsaye a yankin Hong Kong wadanda suka hada kai da sauran bangarorin kasashen waje. (Zainab)