logo

HAUSA

Shugaban Kenya ya yaba da tagwayen hanyoyin da kasar Sin ta gina a Nairobi

2021-12-24 09:39:55 CRI

Shugaban Kenya ya yaba da tagwayen hanyoyin da kasar Sin ta gina a Nairobi_fororder_211224-I1.Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya yaba da tagwayen hanyoyi na zamani da kasar Sin ta gina a Nairobi, babban birnin kasar, a matsayin wani muhimmin aikin samar da ababen more rayuwa.

Kenyatta ya ce, tagwayen hanyoyin za su rage cunkoson ababen hawa da mutane suke fuskanta, wanda hakan ya kara tsadar harkokin kasuwanci a kasar.

Shugaba Kenyatta ya yi nuni da cewa, tagwayen hanyoyin sun samar da ayyukan yi kai tsaye sama da 6,000, baya ga ’yan kwangila 200 da kuma daruruwan masu samar da kayayyakin gini na cikin gida kamar karafa, da yashi, da siminti da duwatsu, da roduna, da su ma suka amfana.

Shugaban na Kenya ya musanta ikirarin cewa, wai alakar Kenya da Sin ba ta da wani amfani. Yana mai cewa, mutane da dama sun shaida mana cewa, wai dangantakarmu da kasar Sin ba ta da wani amfani. Ga wadanda suka fadi haka, ina rokonsu da su zo, su ga irin wannan aikin.

Kenyatta ya tabbatar da aniyar kasarsa ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin kasar Sin, yayin da take ci gaba da kasancewa babbar aminiyar raya kasa.

Ya lura cewa, kasar Sin ta gudanar da ayyuka da shirye-shirye da dama, wadanda suka kyautata rayuwar jama'ar Kenya. (Ibrahim Yaya)