logo

HAUSA

An samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da COVID-19 cikin kwana guda a Nijeriya

2021-12-24 10:12:19 CRI

An samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da COVID-19 cikin kwana guda a Nijeriya_fororder_211224-I2-Najeriya

Hukumomin lafiya a Nijeriya, sun ce kasar ta samu sabbin mutane 4,035 da suka kamu da COVID-19 a ranar Laraba, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka samu cikin kwana guda, tun bayan bullar cutar a karon farko cikin watan Fabrerun 2020.

Lagos dake zaman cibiyar kasuwanci ta kasar kuma inda aka fara samun bullar cutar, ita ce ta dauki adadin masu cutar 3,393 cikin wadanda suka kamu a ranar Laraba.

Shugaban hukumar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta kasar NCDC Ifedayo Adetifa, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kasar ta yammacin Afrika na fuskantar barkewar cutar a karo na 4, yana mai alakanta hakan da karuwar nau’ikan cutar na Delta da Omicron.

Shi kuwa shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na kasar, Faisal Shuaib, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, kawo yanzu, sama da mutanen Nijeriya miliyan 10 sun karbi alluran riga kafi. Yana mai cewa kasar na da alluran da za su wadaci al’ummarta.

Alkaluman hukumar NCDC sun nuna cewa, da wannan adadi da aka samu a ranar Laraba, jimlar wadanda suka kamu da cutar a kasar ta kai 231,413. Daga cikinsu kuma, mutane 211,853 sun warke, yayin da 2991 suka mutu. (Fa’iza Mustapha)