Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Shugaban Kasar Gambia
2021-12-24 20:23:52 CRI
A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Gambia Adama Barrow, bisa sake zaben sa da aka yi a matsayin shugaban kasa.
Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce tun bayan dawo da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Gambia, sassan biyu ke zurfafa amincewa ta fuskar siyasa, sun kuma cimma manyan nasarori a fannonin hadin gwiwar su, kaza lika sun fahimci juna, tare da taimakawa juna a dukkanin al’amuran dake shafar manyan muradun su.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yana dora matukar muhimmanci kan ci gaban dangantakar sassan biyu, kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki da bangaren Gambia, wajen zurfafa hadin gwiwa da mahukuntan kasar, da ma hadin gwiwar kasar sa da sassan Afirka, karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, ta yadda Sin da Gambia da al’ummun su, za su ci gaba da cin gajiyar dangantakar su. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Shugaba Xi ya aike da sakon ta’aziyyar wadanda mahaukaciyar guguwar Rai ta halaka a Philippines
- Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Yankin Tattalin Arziki Na Musamman Na Xiamen
- Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin karfafa dokokin jam’iyya domin kare jagoranci da gudanar da gwamnati cikin nasara
- Shugaba Xi Ya Gana Da Wakilan Al’umma Masu Ba Da Gudummawa Ga Wanzar Da Zaman Lafiya A Sin