logo

HAUSA

Kasar Sin ta bayyana adawa da dokar “haramta kwadago bisa tilas ta Uygur” da Amurka ta yi

2021-12-24 11:50:28 CRI

Kasar Sin ta bayyana adawa da dokar “haramta kwadago bisa tilas ta Uygur” da Amurka ta yi_fororder_211224-F3-Xinjiang

Kasar Sin ta bayyana adawa da matakin Amurka na zartar da dokar da ta kira, “haramta tilastawa al’ummar Uygur kwadago”, tana mai bayyanata a matsayin wadda ta yi watsi da gaskiya, sannan ta keta yanayin hakkin bil adama na jihar Xinjiang ta kasar Sin. Haka kuma dokar ta take dokokin kasa da kasa da ka’idojin huldar kasa da kasa, tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce batutuwan da suka shafi Xinjiang, ba batutuwa ne na hakkin bil adama ba, batutuwan ne da suke yaki da ta’addanci da rikici da zancen ballewa. Ya ce Sin na shaidawa Amurka cewa, amfani da batutuwan da suka shafi Xinjiang domin kulla munafurci, ba zai hana al’ummar dukkan kabilun dake jihar neman rayuwa mai inganci ba, haka kuma ba zai dakatar da Sin daga samun ci gaba ba.

A cewarsa, matakin na Amurka ya sabawa ka’idojin kasuwa da na kasuwanci, wanda kuma zai kawo tsaiko ga ayyukan masana’antu a duniya da tsarin samar da kayayyaki da tsarin cinikayya na duniya, da kuma lalata muradun ita kanta Amurkar da kimarta.

Har ila yau, ya nanata cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, batutuwa ne na cikin gidan Sin. Kuma kudurin gwamnati da al’umma na kare cikakken ’yanci da tsaro da ci gaban kasar, ba zai sauya ba. A don haka, Sin na kira ga Amurka, ta gaggauta gyara kura-kuranta, ta kuma daina amfani da batun wajen baza karairayi da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin da nufin dakile ci gabanta. Bugu da kari, ya ce Sin din za ta mayar da martani bisa la’akari da yanayin batun. (Fa’iza Mustapha)