logo

HAUSA

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021

2021-12-23 14:00:58 CRI

 

Daga Amina Xu

Shekarar 2021 na da babbar ma’ana ga Sin da Najeriya, shekara ce ta cika shekaru 50 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakaninsu. Shin wadanne nasarori ne kasashen biyu suka cimma a hadin gwiwarsu a wannan shekara?

Najeriya ta kasance daya daga cikin abokan hadin gwiwar kasar Sin a nahiyar Afirka, a dangantaka bisa manyan tsare-tsare, kuma hadin kansu na sahun gaba a hadin kan Sin da kasashen Afrika, musamman ma layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna da yankin ciniki cikin ‘yanci na Ogun da fannin harba tauraron dan Adama da hadin kai a fannin binciken teku da dai sauransu, suna daga cikin hadin kai irinsu na farko a Afrika.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Sin, ya kan kai ziyararsa ta farko a nahiyar Afrika a farkon kowace shekara, a wannan shekara ma, Wang Yi kai ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka, kuma ya mai da Najeriya zangonsa na farko a ziyarar, abin da ya bayyana cewa, Sin tana dora babban muhimnanci kan bunkasuwar dangantakar Sin da Najeriya. A yayin ziyararsa, Wang Yi ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kuma ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, inda suka kai ga cimma matsaya daya a bangarori daban-daban.

Bari mu duba yadda aka tabbatar da matsayar da aka cimma a wannan shekarar 2021 da ke karewa.

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021_fororder_9f510fb30f2442a76e9142762d200643d0130236

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021_fororder_9a504fc2d5628535a9a9bfd2198a2ccfa6ef6362

 

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021_fororder_a8014c086e061d951dd1226dad3d19d863d9ca26

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021_fororder_20210922102032482

Dangantakar Sin Da Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunkasuwa A Shekarar 2021_fororder_bab444da70e74c3499b7b3ab88d283fb

A watan Jarairu, gwamnatin Sin ta kaddamar da shirin raya kauyukan Afrika fiye da dubu 10 wajen kama shirye-shiryen talabijin na zamani a Najeriya. A watan Mayu, Madatsar ruwa ta Zungeru dake samar da wutar lantarki da kamfanin Sin ya taimaka wajen gina ta, ta fara tara ruwa, matakin da ya share fage ga aikin samar da wutar lantarki da za a gudanar a karshen wannan shekara, aikin da zai magance matsalar karancin wutar lantarki da Najeriya ke fuskanta, da kyautata zaman rayuwar al’ummar. Ban da wannan kuma, A watan Yuni, an fara amfani da layin dogon dake tsakanin birnin Lagos da Ibadan da kamfanin Sin ya tamaka wajen gina shi, wanda ya kasance wani muhimmin mataki daga cikin shirin bunkasa layukan dogo na zamani na Najeriya, a watan Yuli kuma, kamfanin Sin ya fara aikin shimfida layin dogo dake tsakanin Kaduna zuwa Kano, wanda ya kasance wani muhimmin bangare na tsarin layukan dogo na Najeriya, wanda gwamnatin Najeriya ta ba da babban muhimmanci kan wannan aiki. Dadin dadawa, a watan Oktoba, kamfanin Sin ya kammala aikin gina tashar jiragen sama na jihar Anambra.

Wadannan ayyuka, wani kashi ne daga cikin hadin kan Sin da Najeriya, Sin a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a duniya, yayin da Najeriya ke zama kasa mafi yawan al’umma a Afrika, dukkansu kasashe ne masu tasowa, suna da makoma mai haske wajen hadin kansu da cin moriya tare. Kasashen biyu sun samu ci gaba mai armashi a hadin gwiwarsu a wannan shekara, duk da cewa al’ummar duniya ke ci gaba da fama da cutar COVID-19 . Dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da aka gudanar a watan Nuwamban wannan shekara, ya karawa bangarorin biyu kwarin gwiwa a hadin kansu nan gaba. Ba shakka, a cikin shekara mai zuwa, huldar Sin da kasashen Afrika ciki hadda dangantakar Sin da Najeriya, za ta samu bunkasuwa zuwa wani sabon matsayi, abin da zai amfanawa al’ummar kasashen biyu. Yayin da muke ban kwana da shekarar 2021, tare da shirin shiga sabuwar shekara ta 2022. Muna fatan sabuwar shekara, za ta kasance mai cike da alharei ga bunkasuwar huldar Sin da Najeriya. (Amina Xu)