logo

HAUSA

Kasuwar Sassa Masu Fitar Da Iskar Carbon Ta Sin Ta Kai Darajar Yuan Biliyan 5.8

2021-12-23 20:47:57 CRI

Kasuwar Sassa Masu Fitar Da Iskar Carbon Ta Sin Ta Kai Darajar Yuan Biliyan 5.8_fororder_sin

Kasuwar sassan dake fitar da nau’o’in iskar Carbon mai dumama yanayi ta kasar Sin, ta kai darajar kudin kasar yuan biliyan 5.8, kwatankwacin dalar Amurka mliyan 911.53.

Ma’aikatar lura da muhallin halittu ta kasar ko MEE a takaice, ta bayyana a Alhamis din nan cewa, ya zuwa jiya Laraba, kasuwar sassan dake fitar da iskar Carbon a kasar, ta yi cinikayyar da ta kai tan miliyan 140, tun bude hada hadar ta a ranar 16 ga watan Yuli.

A matsayin ta na jigon kirkire-kirkire na kasar Sin a fannin rage fitar da nau’o’in iskar Carbon, a yanzu haka kasuwar ta kunshi kamfanonin samar da makamashi 2,162, wadanda ke fitar da iskar carbon dioxide har tan biliyan 4.5 a duk shekara.

Ana sa ran shigar da karin wasu sassan dake fitar da iskar Carbon cikin wannan rukuni a nan gaba, a kokarin da ake yi na cimma burin kasar Sin, na rage fitar da nau’o’in iskar Carbon.

Kasar Sin ta sanar da aniyarta, ta kaiwa kololuwar fitar da iskar carbon dioxide ya zuwa shekarar 2030, da kuma samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060.  (Saminu)

Saminu