logo

HAUSA

Tawagar ma’aikatan kiyaye tsaron al’ummar Sinawa ta tattauna da sufeton ‘yan sandan Najeriya

2021-12-23 10:48:00 CRI

Tawagar ma’aikatan kiyaye tsaron al’ummar Sinawa ta tattauna da sufeton ‘yan sandan Najeriya_fororder_7042106340856791047

Jiya ne, shugaban tawagar hukumar kiyaye tsaron al’ummar Sinawa Yin Guohai, ya tattauna da Usman Baba Alkali, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya a hedkwatar ‘yan sandan Najeriya. Yayin ganawar, Yin ya nuna cewa, Sin da Najeriya na da daddaden zumunci a tsakaninsu, kuma bangarorin biyu na kara tuntubar juna a ko da yaushe, an kuma samu ci gaba mai armashi a hadin gwiwar sassan a bangarorin daban-daban. Ya kara da cewa, Sinawa da dama na zuba jari da gudanar da ayyukansu a Najeriya, matakin da ya ba da gudunmawa wajen raya tattalin arziki da jin dadin al’ummar Najeriya. Haka kuma gwamnatin Sin na dora babban muhimmanci kan tsaron Sinawa dake kasar, tana kuma fatan gwamnatin Najeriya, za ta dauki matakan da suka dace, don dakile aikata munanan laifuffuka, ta yadda hakan zai ba da tabbaci ga tsaro da hakkin Sinawa dake kasar.

A nasa bangare, Usman Baba Alkali ya ce, kasashen biyu na da dankon zumunci na dogon lokaci. Kuma Najeriya na dora babban muhimnanci kan huldar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce, Najeriya na maraba da karawa Sinawa kwarin gwiwa, don su gudanar da ayyukansu a Najeriya, ta yadda za a ingiza bunkasuwar huldar bangarorin biyu. Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta kara karfin tabbatar da tsaron Sinawa dake kasar. Yana kuma fatan kara hada kai da Sin ta fuskar ayyukan ‘yan sanda. (Amina Xu)