logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da gwamnar kantomar Hong Kong da kantoman yankin Macao

2021-12-22 21:39:56 CRI

Xi Jinping ya gana da gwamnar kantomar Hong Kong da kantoman yankin Macao_fororder_1222-02

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da kantomar yankin Hong Kong Carrie Lam, da kantoman yankin Macao Ho Iat Seng da suka zo birnin Beijing don yin bayani kan ayyukansu a yammacin yau.

Yayin ganawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin shekara daya, an canja yanayin zaune tsaye zuwa yanayin zaman lafiya a yankin Hong Kong. Ya ce ana cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, da farfado da tattalin arziki, da kuma kiyaye zaman lafiya a zamantakewar al’umma a Hong Kong. A nata bangare kuma, Carrie Lam ta jagoranci gwamnatin yankin Hong Kong, da kyautata tsarin zaben yankin bisa kudurorin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da dokokin da aka zartas a zaunannen kwamitin majalisar, da gudanar da zaben kwamitin yin zaben da hukumar tsara dokokin yankin cikin nasara, wadanda suka dace da hanyar bunkasa demokuradiyya a yankin. Kana an aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa a yankin, da hana faruwar rikice-rikice bisa doka, da tabbatar da dokokin yankin.

Yayin da shugaba Xi yake ganawa da Ho Iat Seng kuwa, ya yi nuni da cewa, a cikin shekara daya da ta wuce, an kiyaye samun bunkasuwa a yankin Macao yadda ya kamata. An cimma nasarar magance yaduwar cutar COVID-19, da yin mu’amala da mutanen babban yankin kasar Sin yadda ya kamata. Kana ana kyautata tsarin dokoki, da tsarin daukar matakai don tabbatar da tsaron kasa a yankin. An kammala zaben hukumar tsara dokoki ta yankin karo na 7 cikin nasara, ta haka an bi ka’idar maida masu kishin kasa su tafiyar da harkokin yankin Macao. (Zainab)