Adadin wadanda ‘yan bindiga suka hallaka a Kaduna sun kai mutum 38
2021-12-20 20:26:56 CRI
Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, ta ce adadin wadanda suka rasu sakamakon harin ‘yan bindiga a wasu kauyuka 3 a karamar hukumar Giwa sun karu zuwa mutum 38.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce maharan sun aukawa kauyuka 3 da daren Asabar, da kuma safiyar Lahadi.
Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin na Kaduna, yana mai bayyana lamarin da mummunar ta’asa da ta yi matukar tayar masa da hankali. Shugaba Buhari ya kuma jaddada umarnin da ya baiwa dakarun tsaro, da shugabannin hukumomin leken asiri, na su yi dukkanin mai yiwuwa wajen kakkabe gyauron ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Najeriya ta ce sojojinta sun kashe mayakan IS da dama
- Najeriya ta janye dakatarwar da ta yiwa kamfanin jiragen saman Emirates
- Masanin Najeriya: Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Wadatar Da Kowa A Kasar Ya Cancanci Kasashe Masu Tasowa Su Koya
- Najeriya ta doke Liberia inda take dab da yin nasara a share fagen shigar gasar cin kofin duniya