logo

HAUSA

Zhou Yasong: Cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da ‘yarta

2021-12-17 09:41:05 CRI

Zhou Yasong: Cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da ‘yarta_fororder_周亚松4

A kasar Sin, iyaye ba sa watsi da kokarin cimma burikansu, in ma burin na kara ilimi ne ko fara sabon aiki. Wadannan iyaye mata masu yara, sun yi kokarin cimma burikansu kuma sun yi rayuwarsu yadda suke so. Ta hakan, sun kuma haskaka rayuwar ‘yayansu.

Burin uwa kan yi tasiri a kan rayuwar ‘ya’yanta, kuma yana kara nunawa ‘ya’yan hanya mafi dacewa tare da bayar da kwarin gwiwa da kuma karfi.

Zhou Yasong mai shekaru 56, wadda ta yi wani kwas na neman digiri na biyu a jami’a daya da ‘yarta Wu You, ta samu izinin fara karatun digiri na 3 daga jami’ar Jamhuriyar Koriya a ranar 1 ga watan Yuli. Labarin ya yi ta yawo a kafar intanet, inda aka yi ta yabawa Zhou a mastayin mai kokarin cimma burinta. Zhou ta amsa cewa, “buri na ne, kuma sakamakon kokarin da na yi ta yi ne, har yanzu da sauran tafiya a gaba”.

Zhou ‘yar asalin Changde na lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin, ta yi aiki a matsayin mai tattarawa da adana bayanai a wani ofishin gwamnatin karamar hukuma. ‘Yarta ta bude mata wani dakin wake-wake a shekarar 2013, domin koyar da dabarun waka da fiyano ga yara.

Shekaru biyu bayan nan, Wu ta fara shirin rubuta jarrabawar yin karatun neman digiri na biyu, kuma ta tsara burin da take son cimmawa, wato karatu a sashen nazarin wake-wake na Jami’ar ilmantar da malamai ta birnin Wuhan na lardin Hubei, dake tsakiyar kasar Sin.

Domin rage ayyukan dake gaban ‘yarta, Zhou kan raka Wu lokacin da take koyon waka da yin jarrabawa da daukar darasi. Daga bisani, ita ma ta yanke shawarar daukar jarabawar.

Zhou Yasong: Cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da ‘yarta_fororder_周亚松2

Rubuta jarrabawar ba buri ne na rana guda ba a wajen Zhou. Bayan kammala makarantar sakandare, Zhou ta samu gurbin karatu a wata kwalejin nazarin fasaha, amma dole ta hakura saboda iyayenta ba za su iya daukar nauyinta ba. Kakan Zhou masanin wakokin gargajiya ne, wanda ke iya amfani da kayayyakin waka da kida da dama, kuma ya yi tasiri a kan Zhou. Saboda tasirinsa, Zhou ta girma tana kaunar wake-wake, kuma ta koyi yin waka da rawa da buga fiyano da wasu kayayyakin kida.

Cikin shekaru sama da 30, Zhou ta yi ta koyon dabarun waka da motsa jiki a lokacin da ba ta da wani aikin da za ta yi. Duk da cewa ta haura shekaru 50, tana iya yin wasu atisayen. Ta kammala karatun digiri ta hanyar wani shirin “koyo da kanka” da wata jami’a ta gabatar.

A lokacin da take gab da ritaya, ta yanke shawarar kara gwada cimma burinta na kammala koyon waka a wata fitacciyar makaranta.

“Ban damu da digiri ba…amma ina kaunar sake zama daliba”, cewar Zhou. Ta ce tana son ‘yarta ta san cewa mata na iya kokarin cimma burikansu ta hanyar dagewa.

Wasu mutane sun bayyana shakku game da kudurin Zhou. “mabanbanta mutane na da ra’ayi mabanbanta. Ina son koyon abubuwa. Koyon abubuwa tsawon rayuwata ne kadai zai gamsar da ni” cewar Zhou. Wu ma ta amince da hakan. Ta yi ta karfafawa mahaifiyarta gwiwa. Wu ta shaidawa mahaifiyarta cewa, “ ki yi abun da kike so, kuma ki yi abun da ya dace da zai saki farin ciki.”

Bayan yanke shawara, Zhou ta gaggauta yin ritaya sannan ta shirya tafiya tare da ‘yarta don rubuta jarrabawar. Zhou da Wu, sun kama hayar gida a kusa da Jami’ar ilmantar da malamai ta tsakiyar kasar Sin, kuma tare suke daukar darasin shiryawa jarrabawar.

Zhou Yasong: Cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da ‘yarta_fororder_周亚松3

A watan Afrilun 2016, Zhou ta shiga jami’a, sai dai ba a dauki ‘yarta ba. “har yanzu da kuruciyarki. Kina da sauran dama,” cewar Zhou, domin karfafawa Wu gwiwa, wadda a kullum ke ganin mahaifiyarta a matsayin tushen kwarin gwiwarta.

A ranar 1 ga watan Satumban 2016, Zhou ta fara rayuwar da ta dade tana buri, wato goya jaka domin shiga aji da cin abinci a dakin sayar da abinci na makaranta da kwanciya a kan gadon dakin kwanan dalibai da karatu a dakin karatu.

Zhou na yawaita furuta kalaman da za su sanyaya zuciyar ‘yarta, kuma ta kan fada mata yadda rayuwarta ke kasancewa yayin rubuta jarrabawa. Shekara daya bayan nan, Wu ta samu gurbin karatu a jami’ar.

Duk da cewa suna zama a dakin kwanan dalibai daya, karatu ba ya bari su rika haduwa akai-akai. Wani lokacin su kan ci abinci tare a dakin cin abinci, kuma idan suna tare, su kan shafe lokacin suna hira da dariya.

Zhou ita ce mafi girma kuma mafi kwazo a ajinsu. Ta kan tashi da misalin 6 na safiya a kowacce rana don buga fiyano. Wu na taimaka mata da darrusa masu wahala. “a gaskiya, ina daukar lokaci fiye da matasa kafin in koyi abu. Amma da zuciya mai karfi da lafiya, zan iya tafiya tare da su”, cewar Zhou.

Zhou Yasong: Cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da ‘yarta_fororder_周亚松5

Yanzu an dauki Wu aiki a wata kwaleji a lardin Hunan. Tana koyar da dabarun rera waka. Idan tana magana kan mahaifiyarta, tana yawaita amfani da kalmomin “kauna” da “dagewa” . A gare ta, a kullum Zhou na da kyakkyawar fata, da kwarin gwiwa ba tare da gajiyawa ba.

“Ina son wake-wake, kuma zan ci gaba da koyo. Zan ci gaba da kasancewa aminiyar ‘yata. Ina son shaida mata cewa, muddin za ta jajirce kan cimma burinta, to za ta yi nasara, nan ba da dadewa ba. Abun da ba ya shafi shekaru ba ne,” cewar Zhou.

Kande