logo

HAUSA

Kar‘Yan Siyasar Amurka Su Cuci Jama’a Da salon Demokuradiyyarsu

2021-12-16 19:23:08 CRI

图片默认标题_fororder_QQ图片20211216191822

Jama’a, a ra’ayinku mene ne ainihin demokuradiyya? Kwanan baya, an kawo karshen taron kolin da Amurka ta kira da sunan wai demokuradiyya. ‘Yan siyasar Amurka su kan kira kasarsu kasar da ta fi dadadden tarihi ta fannin wanzar da Demokuradiyya, amma shin ko da gaske ne tana da Demokuradiyya?

A shekarar 1787, wadanda aka kira su masu kafa kasar Amurka sun yi taro a birnin Philadelphia don tsara tsarin mulkin kasar Amurka. Jagoran kafa tsarin mulkin Amurka James Madison ya ce, dole ne a kafa gwamnatin dake iya kiyaye moriyar masu wadata, ta yadda ba za a kawo musu barazana ba. Ban da wannan kuma, shahararren mai ba da gudunmawa wajen kafa kasar Amurka Elbridge Gerry ya yi ikirarin cewa, laifukan da aka aikata mana demokuradiyya ce ta haddasa su. Bisa la’akari da abubuwan da wadannan sharararrun mutane a tarihin Amurka suka fadi, muna iya ganin cewa, ‘yan siyasar Amurka ba su son demokuradiyya ko kadan, inda kawai suke son kiyaye moriyar masu wadata. Wannan taro mai nuna kiyayya ga demokuradiyya, da yunkurin kiyaye moriyar masu wadata, ya kafa wani tsarin mulki ba tare da ambatar demokuradiyya ko kadan ba. To ko ta yaya Amurka za ta cancanci sunan “Tsohuwar kasa mai bin demokuradiyya”?

A halin yanzu, demokuradiyya ta zama ra’ayin Bil Adam na bai daya, hakan ya sa wasu shugabannin Amurka suke yawan magana a kan batun dimokuradiyya. Jama’a na matukar fatan samun ikon gudanar da harkokin kasarsu, da tabbatar da hakkinsu, da samun daidaito, amma hakan ba zai yiwu ba a wurin gwamnati mai tafiyar da harkokinta bisa tunanin kiyaye moriyar masu wadata kawai.

A zamanin masu jarin hujja, masu wadata na yunkurin kiyaye dukiyoyinsu, don haka suka rungumi “’yanci”, sai dai a wannan lokaci demokuradiyya ta kawo cikas ga burinsu. Abin da ya haifar da juyin juya hali da ma’aikata suka yi. Don haka, ‘yan siyasa sun fitar da wata manufa don kare mulkinsu, wato mai da demokuradiyya a matsayin ikon kada kuri’a. Hakan tamkar ya baiwa jama’a hakki na gudanar da harkokin kasar, amma a hakika wannan abu ne da suke kira “Demokiradiyya”. Hakkin da jama’a ke da shi na kada kuri’u kawai, bayan zabe ba ruwansu da demokuradiyya. Ba shakka, ‘yan siyasar Amurka ba su kawo hakikanin amfani ga jama’a don biyan bukatunsu na demokuradiyya ba ko kadan.

Game da demokuradiyya iri ta Amurka, wasu kafofin yada labarai da binciken jin ra’ayin jama’a da aka yi game da hakan, sun yi nazari a kan aibobinta. ‘Yan siyasar Amurka sun dade sun mai da  demokuradiyya a matsayin hakkin kada kuri’u, kuma bisa wannan ma’auni ne suke tantance sauran kasashe kan cewa ko suna da demokuradiyya ko a’a, amma tsarin kada kuri’u na Amurka ba tsari ne mai kyau ba, ba ma kawai jama’a ba su da hakki cikin daidaito a wannan fanni ba, har ma ba a gudanar da harkokin zabe yadda ya kamata ba, hakan ya sa sakamakon zabe ya kara gaza samun amincewa daga jama’a. ‘Yan siyasar Amurka kar ku nuna kamar ba ku san bambanci tsakanin ainihin demokuradiyya da demokuradiyya iri ta Amurka ba, domin jama’a na da fahimta sosai kan hakan. (Amina Xu)