logo

HAUSA

Idan Muka Kalli Alkaluma Biyu, Ta Yaya Amurka Za Ta Fake da "Dimokuradiyya "?

2021-12-14 21:25:26 cri

Idan Muka Kalli Alkaluma Biyu, Ta Yaya Amurka Za Ta Fake da "Dimokuradiyya "?_fororder_微信图片_20211214200909

Ya zuwa ranar 13 ga wata bisa agogon wurin, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 50, kuma adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 800,000, wanda ya kasance a kan gaba a duniya. Wani rahoto da aka wallafa a shafin yanar gizo na "USA Today" a ranar 9 ga wata, ya nuna cewa, an rage adadin wadanda suka mutu da akalla kashi 20%, wato mai yiwuwa adadin ya ya wuce miliyan 1.

Me ya sa kasar da ta fi ci gaba a duniya ta zama kasa ta farko da ta gaza wajen yaki da annobar? Me ya sa Amurka, wacce ke alfahari da kanta a matsayin "Abin koyi a tsarin dimokuradiyya," ba za ta iya ba da tabbacin yancin rayuwar jama'arta ba?

Domin ganin ya lashe babban zaben kasar, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da daukar matakan rigakafin annobar ta hanyar kimiyya, tare da fifita muradun siyasa sama da rayuwar mutane. Kana shi ma shugaban kasar na yanzu Joe Biden ya tsunduma cikin abin da ake kira aikin gano asalin cutar domin siyasa, yana mayar da hankali kan dora laifi kan sauran kasashe, wanda ya kawo cikas ga ci gaban yunkurin yakar annobar a kasar ta Amurka.

Ban da wannan kuma, matsalar nuna wariyar launin fata da ta dade tana faruwa a kasar Amurka, ita ma ta ta'azzara saboda yaduwar annobar.

Kamar yadda jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta yi nuni da cewa, Amurka ta bar tsarin kula da lafiya mai tsada ga masu hannu da shuni, ta kuma kwace tsarin samun lafiya na talakawa. Wannan ya zama misali na rashin iya shawo kan cutar yadda ya kamata saboda saba wa demokradiyya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)