logo

HAUSA

Chen Lu, wadda ke kokarin taimakawa duniya wajen gano nishadin dake tattare da wasan tsalle da zamiyar kankara.

2021-12-07 17:10:21 CRI

Chen Lu, wadda ke kokarin taimakawa duniya wajen gano nishadin dake tattare da wasan tsalle da zamiyar kankara._fororder_21104682

Madam Chen Lu da ta yi suna a matsayin Butterfly on Ice wato malam-bude-littafi a kan kankara, saboda kwarewarta a wasan tsalle da zamiyar kankara, ta zama Basiniya ta farko da ta zama zakarar duniya a wasan a 1995. Haka kuma ta samu lambar Tagulla a wasannin Olympics na lokacin hunturu na Lillehammer na kasar Norway a 1994 da na Nagano na Japan na shekarar 1998. Duk da ta yi ritaya daga kungiyar wasan tsallae da zamiyar kankara ta kasar Sin a 1998, Chen ba ta taba daina kokarin taimakawa duniya wajen gano nishadin dake tattare da wasan zamiyar kankara ba. Cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, ta yi kokarin horar da kananan ‘yan wasan kankara da taimakawa jama’a fahimtar wasan.

An haifi Chen Lu ne a iyalin ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Changchun, babban birnin Lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin a shekarar 1976. Wasanni a cikin jininta yake tun tana ‘yar karama. Babanta Chen Xiqin, yana wasan kwallon gora a kan kankara, mahaifiyarta Cui Yan kuma, tana buga kwallon tebur. Lokacin da take karama, Chen Lu na son zuwan filin wasan zamiyar kankara a kusa da gidansu. Lokacin da take shekara 4, iyayenta suka tura ta wata makarantar wasanni a Nanguan, wani yanki a birnin Changchun, don koyon fasahar tsalle da zamiyar kankara, ta yadda za ta kasance cikin koshin lafiya da kyan jiki. Yayin da take shekaru 6 zuwa 11, Chen Lu ta kere dukkan abokan karawarta yayin gasar wasan tsalle da zamiyar kankara ta yara ta lardin Jilin. Da ta cika shekaru 13 da haihuwa, ta zama zakarar kasar Sin a karon farko, wadda ta kasance daya daga cikin lambobin zinari goma na kasar Sin da ta samu gaba daya.

Chen Lu tana jinjinawa mahaifinta, wanda ya taimaka mata wajen inganta kwarewarta ta wasan tsalle da zamiyar kankara. A lokacin da take karama, mahaifinta yana kallon yadda take wasa a kullum. Ya kan dauki dabaru daga littattafai da bidiyo kan manyan masu wasan, domin taimakawa Chen Lu inganta kwarewata.

A matsayin matashiya ‘yar wasan tsalle da zamiyar kankara, a farkon 1990, Chen Lu ta nuna kwarewarta na wasanni da fasaha. Duk da nasarorin da ta samu a farkon sana’arta, ta kan shiga fargaba idan ta hadu da abokan karawa daga kasashen Turai da Amurka yayin wasannin kasa da kasa. Sai dai, wannan Basiniya ta burge duniya da hazakarta. Misali, ta zo ta uku a gasar cin kofin duniya ta matasa ta wasan tsalle da zamiyar kankara ta 1991 da aka yi a Budapest na kasar Hungary. Lambar Tagulla da ta samu, ita ce lambar yabo ta farko da kasar Sin ta samu a gasar cin kofin duniya ta rukunin mata. A lokacin kuwa, shekarunta sun kai 14 kawai. Ban da wannan kuma, ta samu lambar tagulla a wasan tsalle da zamiyar kankara na wasannin Olympics na lokacin hunturu na Lillehammer a shekarar 1994, wanda ya kasance karon farko da kasar Sin ta samu lambar yabo a wasan a cikin gasar wasannin Olympics.

Chen Lu ta kai matsayin koli a sana’arta ne a 1995, a lokacin da ta lashe gasar cin kofin duniya da aka yi a Birmingham, wanda shi ne irinsa na farko da Sin ta taba lashewa. Hazakarta ta samu yabo matuka. Kuma tun daga sannan ne galibin Sinawa ke mata lakabi da “Ice Queen” wato “Sarauniyar Kankara”.

Sai dai, ba kullum ake kwana a gado ba. Chen Lu ta gamu da shan kaye ne a shekarar 1997, yayin gasar cin kofin duniya a Lausanne na Switzerland. Ta rasa daidaito yayin gasar, inda ta kammala bisa lamba ta 25. A don haka, ba ta samu cancantar shiga gasar a matakin karshe ba. Amma bayan kwarin gwiwar da ta samu daga hukumar kula da wasanni ta kasar Sin, Chen Lu ta samu damar tsallake wannan gabar a rayuwarta.

Ta dawo da kanbunta ne bayan ta ci lambar tagulla yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Nagano da aka yi a 1998. Yanayin wasanta mai salon Butterfly, wato malam bude littafi, shi ne ya samo mata lakabin Butterfly on Ice. Sakamakon haka, ta zama ‘yar nahiyar Asiya mace ta farko da ta samu lambobin yabo a wasannin Olympics biyu na lokacin hunturu.

Chen Lu, wadda ke kokarin taimakawa duniya wajen gano nishadin dake tattare da wasan tsalle da zamiyar kankara._fororder_21104680

Wasan tsalle da zamiyar kankara ya kasance sana’ar da Chen Lu take kauna a rayuwarta. Jim kadan bayan ta yi ritaya daga kungiyar wasan ta kasar Sin a 1998, ta fara wasa a kungiyar zamiya ta San Francisco na Amurka. A wancan lokaci, Chen Lu ta koyi fasahar wasan kwaikwayo, da ma yadda ya kamata a yi kasuwanci a filin zamiyar kankara. Wannan ya shimfida tubali ga makomar sana’arta ta kafa kungiyoyin zamiyar kankara a kasar sin, domin yayata dabaru da gogewarta ga sauran ‘yan wasa masu tasowa da ma masu sha’awar wasanni.

Cikin shekarun da suka biyo baya, Chen Lu ta shiga yankuna da dama na Amurka. A shekarar 2004 kuma, ta sayar da gidanta da mota dake Maryland na Amurkar, domin dawowa kasar Sin. Jim kadan a bayan nan, ta samu aiki da wani kamfani domin tafiyar da harkokin wuraren zamiyar kankara na kasuwanci a Shenzhen, wani birni dake lardin Guangdong na kudancin kasar Sin. Maimakon more rayuwa a Amurka cikin sauki, ta zabi hanya mai cike da wahala. Kuma ba ta taba nadamar tafarkin da ta zaba ba.

Jim kadan bayan ta bar aiki da kamfanin birnin Shenzhen a 2014, Chen Lu ta kafa kungiyoyin zamiyar kankara a Beijing da Shenzhen da wasu yankuna da dama na kasar Sin. Cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ta yi ta yayata wasan zamiyar kankara a tsakanin Sinawa, musamman matasa. Ta yi amfani da abun da ta koya a Amurka wajen horas da kananan ‘yan wasa da kuma tafiyar da kungiyoyin.

“Wasan tsalle da zamiyar kankara sana’a ce da nake kauna. Zan kara kokarin kira ga matasa su shiga wasan, a sannan, zan yi alfahari da ganin cikar burina, zan yi kokarin yayata wasan tsalle da zamiyar kankara na kasata, domin sakawa al’umma da irin kulawa da taimakon da suka min,” cewar Chen Lu.

Tsakanin shekarar 2004 da 2017, Chen Lu ta shirya rangadin wasan tsalle da zamiyar kankara a manyan biranen kasar Sin da dama. Ta kuma jagoranci masu wasan daga wani kamfani na birnin Shenzhen, yayin wata rawar kan kankara a bikin bude wasannin lokacin hunturu na kasar Sin karo na 13 da aka yi a watan Junairun shekarar 2016 a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar.

A shekarar 2005, Chen Lu ta auri Denis Petrov, dan kasar Rasha, kuma dan wasan tsalle da zamiyar kankara da ya samu lambar azurfa tare da abokiyar wasansa a wasannin Olympics na lokacin hunturu na Albertville na kasar Faransa da aka yi a shekarar 1992. Chen da Petrov suna da ‘ya’ya biyu, mace da namiji. Diyarsu Anastasia Petrov, ta yi gadon mahaifanta. Yarinyar mai shekaru 11 yanzu, ta bi sawun mahaifiyarta. Anastasia ta lashe gasar wasan tsalle da zamiyar kankara ta yara ta nahiyar Asiya da aka yi a Beijing, a shekarar 2017.

Cibiyar wasan zamiyar kankara ta kasa da kasa ta Chen Lu tana jan hankali tun bayan bude ta a Beijing a lokacin bazara na 2017. Ba horar da masu sha’awar wasanni kadai cibiyar ke yi wajen taimaka musu inganta wasannin zamiya da kwallon gora a kan kankara ba, har da taimakawa ‘yan wasan kungiyar zamiyar kankara ta kasar Sin inganta kwarewarsu. Zuwa shekarar 2019, ta bude rassan cibiyar a Dalian da Tianjin. Ana sa ran bude na Shenzhen, nan gaba a bana.

A jajibirin kirismeti a shekarar 2020, Chen Lu ta shirya matasan kungiyarta na Beijing su yi wasa kyauta domin nishadantar da yaran dake fama da cutar sankara. An kuma ba da gudumuwar kudi ko kayayyaki, kamar takardu da kayayyakin karatu ga yaran marasa lafiya. “ina fatan matasan masu karbar horo za su taimakawa mabukata”, a cewar Chen.

Chen Lu da Petrov, sun samu ci gaba a sana’arsu na yayata wasan tsalle da zamiyar kankara a tsakanin Sinawa, tun bayan zabar Beijing a matsayin wurin da za a gudanar da wasannin Olympics na lokacin hunturu a 2022. A watan Satumban 2018, kwamitin shirya wasannin Olympics na kasar Sin ya nada Chen Lu a matsayin kocin horar da kungiyar wasan tsalle da zamiyar kankara ta kasar. A matsayinta na mambar kwamitin shirya wasannin Olympics na 2022, Chen na kokarin shirya ‘yan wasa domin gasar. A bana cibiyar wasannin zamiyar kankara ta Chen Lu za ta fara karbar bakuncin wasanni. Cibiyar za ta kuma horar da karin matasa ‘yan wasan tsalle da zamiyar kankara. Chen Lu na fatan karin mutane za su kaunaci wasan, tare da kara fahimtarsa.

Kande