logo

HAUSA

Sin za ta ba da ingantaccen horo ga ma’aikata masu kwarewa

2021-12-02 11:07:30 CRI

Majalisar gudanarwa kasar Sin ta sanar a yayin taronta na ranar Laraba, wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta cewa, kasar za ta gaggauta kokarin ba da ingantaccen horo ga ma’aikatan dake da kwarewa mafi daraja da mutane masu basira.

A yayin taron, an amince da yin sauye sauye a shirin horar da kwarewar sana’o’i da aka amince da su karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025.

A cewar sanarwar, a lokacin kaddamar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13, tsakanin 2016 zuwa 2020, an cimma manyan nasarorin ba da horo ga kwarewar sana’o’i, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaitawa da kuma bunkasa samar da ayyukan dogaro da kai.

Taron majalisar ya ce, za a yi kokarin daukar karin matakai don ba da horo kan kwarewar sana’o’i, wanda zai maida hankali wajen bullo da sabbin hanyoyin samar da ayyukan yi kuma mafiya dacewa da bukatun kasuwannin kwadago da ake da su a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025.

Kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa makarantu da cibiyoyin koyar da sana’o’i da cibiyoyi ba da horo daban daban, taron majalisar ya jaddada muhimmancin bayar da karin tallafi ta hanyar ware wani kaso na kudaden kasafin kudin kasa don giggina sansanonin horar da al’umma.(Ahmad)