logo

HAUSA

Shugaban Afirka ta kudu ya soki lamirin kasashen yamma bisa dakatar da shiga kasashensu saboda bullar sabon nau’in cutar COVID-19

2021-12-02 09:20:17 CRI

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya soki lamirin wasu kasashen yammacin duniya, bisa matakin da suka dauka na dakatar da al’ummun wasu kasashen Afirka daga shiga kasashen su, saboda bullar sabon nau’in cutar COVID-19 na Omicron.

Cyril Ramaphosa, ya bayyana rashin gamsuwar ne a jiya Laraba, yayin taron manema labarai da ya halarta tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Kaza lika shugaba Ramaphosa ya jinjinawa shugaban Najeriya, da takwarorin sa na kasashen Kwadebuwa, da Ghana, da Senegal, bisa nuna rashin amincewar da su ma suka yi da matakin. Ya ce "Wannan annoba ce da ta shafi duniya baki daya, kuma shawo kan tana bukatar hadin kan kowa da kowa”.

Daga nan sai shugaban na Afirka ta kudu, ya bayyana matakin hana shiga kasashen na yamma a matsayin wanda ya sabawa doka, kuma wani nau’in wariya da ba shi da goyon bayan binciken kimiyya, wanda daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba.  (Saminu)