logo

HAUSA

Ba Amurka ce madubin dimokaradiyya ba, in ji ma’aikatar wajen Rasha

2021-12-02 10:16:58 CRI

Ba Amurka ce madubin dimokaradiyya ba, in ji ma’aikatar wajen Rasha_fororder_amurka

A jiya Laraba ne, ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, ta fitar da wata sanarwa dake cewa, ko alama bai dace Amurka ta rika daukar kan ta a matsayin madubin dimokaradiyya ba.

Sanarwar ta ce Amurka da kawayenta, sun gaza wajen magance tarin matsalolin su na cikin gida, da suka hada da na ‘yancin fadin albarkacin baki, da tsara zabuka, da cin hanci, da kare hakkin bil adama.

Kaza lika a cewar sanarwar, shirin Amurka na kiran taron da ta ce wai na kare dimokaradiyya ne, wanda ta tsara gudanarwa tsakanin ranekun 9 zuwa 10 ga watan nan na Disamba, ba komai ba ne illa wani sakon munafurci.

Don haka, sanarwar ta yi kira ga sassan kasa da kasa da kada su amince a yi amfani da su, da sunan kare dimokaradiyya, a haifar da rarrabuwar kawuna. A maimakon haka su maida hankali wajen kare dokokin kasa da kasa, tare da aiwatar da manufofin martaba ikon kasashe na mulkin kai bisa daidaito, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin dokokin MDD. (Saminu)