logo

HAUSA

A kalla mutane 20 sun rasu sakamakon kifewar kwale kwale a Kano dake Najeriya

2021-12-02 10:12:57 CRI

A kalla mutane 20 ne suka rasu galibin su yara ‘yan wata makarantar Islamiyya, sakamakon kifewar wani kwale kwalen da suke ciki, a yankin karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano dake tarayyar Najeriya.

Rahotanni sun ce baya ga wadanda suka rasu, wasu yaran 7 kuma sun jikkata, yayin hadarin kwale kwalen da ya rutsa da fasanjoji kusan 50 da yammacin ranar Talata.

Wata sanarwa da ofishin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fitar, ta ce kwale kwalen ya karye, tare da nutsewa da mutanen dake cikin sa, saboda kazamin lodi na mutane da kayayyaki da ka makare shi da su. Sanarwar ta kara da cewa, mai yiwuwa ne a samu karin mamata, yayin da ake ci gaba da laluben gawawwakin wadanda hadarin ya rutsa da su.

Ana dai yawan samun aukuwar hadarin kwale kwale a Najeriya, sakamakon kazamin lodi, da kuma matsalolin sarrafa jiragen ruwan.  (Saminu)