logo

HAUSA

Putin: Rasha ta gamsu da muhimmin matakin huldarta da kasar Sin

2021-12-01 11:02:54 CRI

Putin: Rasha ta gamsu da muhimmin matakin huldarta da kasar Sin_fororder_putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa, kasar Rasha ta nuna gamsuwa game da matsayin muhimmiyar huldar dake tsakaninta da kasar Sin.

Putin ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a dandalin zuba jari na "Russia Calling".

Da yake tsokaci game da ci gaban kasar Sin, Putin ya bayyana cewa, kasar tana samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma a cewarsa wannan tsari ne dake gudana bisa dacewa wanda ba zai yiwu a dakatar da shi ba.

Shugaba Putin ya kara da cewa, duk wani yunkurin kafa shinge ko sanya takunkumi kan kasar Sin a wannan fannin ba shi da wata hujja kuma ya ci karo da tsarin dokokin kasa da kasa.

Da aka tambaye shi game da makomar manufofin soji na kasar Sin, Putin ya bayyana cewa, kasar Sin tana da ‘yancin kare kanta.

A cewarsa, Rasha ba ta kallon wannan batu a matsayin wata barazana, kana ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin wani muhimmin ginshiki dake ba da gagarumar gudunmawa ga zaman lafiyar duniya.(Ahmad)