logo

HAUSA

Sin da Gabon za su zurfafa amincewa da juna

2021-12-01 21:03:44 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Gabon Pacome Moubelet-Boubeya, sun yi alkawarin zurfafa amincewa da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Wang da Moubelet-Boubeya sun bayyana haka ne a jiya Litinin a gefen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC).

Wang ya ce, a kwanan baya shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da sabbin matakai na samar da taimakon alluran rigakafi ga kasashen Afirka. Kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka, kuma za ta kai alluran rigakafin ga duk wani dan Afirka da ke bukata cikin gaggawa.

A nasa bangare, Moubelet-Boubeya ya bayyana cewa, kasashen Afirka sun samu kwarin gwiwa sosai da muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a bikin bude taron ministocin, jawabin da aike da sako mai kari wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Ibrahim)

Ibrahim