logo

HAUSA

Sin: An tsara wani sabon kundi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka

2021-12-01 20:58:25 CRI

Sin: An tsara wani sabon kundi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka_fororder_focac01

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin da yake amsa tambayoyi da aka yi masa yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa Larabar nan cewa, taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ya cimma sakamako mai kyau, wanda ya nuna cikakken matsayin hadin gwiwar Sin da Afirka, da kuma ci gaban da aka samu tare, da yunkurin Sin da kasashen Afirka na fuskantar kalubale da raba damammaki tare.

Wang Wenbin ya ce, duk da tasirin da sabon nau’in annobar COVID-19 ya haifar, Sin da kasashen Afirka sun shawo kan matsaloli, sun kuma gudanar da taron kamar yadda aka tsara, kana taron ya zartas da Sanarwar Dakar, da shirin Dakar da aka tsara aiwatarwa daga shekarar 2022 zuwa 2024, da Sanarwar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka kan sauyin yanayi da Sanarwar burin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka nan da shekarar 2035. Wannan ya sanya taron zama wanda aka cimma sakamako masu tarin yawa a tarihin dandalin .(Ibrahim)

Ibrahim