logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da ministocin harkokin wajen Guinea da Angola

2021-12-01 10:06:23 CRI

Wang Yi ya gana da ministocin harkokin wajen Guinea da Angola_fororder_angola

Kasashen Sin da Guinea sun sha alwashin zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Guinea, Morissanda Kouyate,  sun lashi takobin zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Wang da Kouyate sun gana a Dakar, babban birnin kasar Senegal ranar Litinin, a gefen taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, karo na takwas.

Wang ya bayyana cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin kasar Guinea ta samu karin moriyar ci gaban kasarta karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika, kana za ta yi aiki tare da kasar Guinea wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da su, domin zurfafa muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Guinea.

A wannan rana kuma, Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Angola, Tete Antonio, inda ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da kuma taimakawa Angola domin kasar ta samu bunkasuwa cikin sauri.(Ahmad)