logo

HAUSA

Peng Liyuan ta gabatarwa ‘yan makarantar Linfen Red Ribbon sakon bidiyo

2021-12-01 14:10:57 CRI

Peng Liyuan ta gabatarwa ‘yan makarantar Linfen Red Ribbon sakon bidiyo_fororder_peng

Yayin da ake bikin ranar kasa da kasa ta yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ko “World AIDS Day” ta bana a Larabar nan, mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta gabatarwa ‘yan makarantar Linfen Red Ribbon sako ta kafar bidiyo.

Cikin sakon na ta, albarkacin bikin na bana wanda shi ne karo 34, Peng Liyuan, wadda kuma ita ce jakadiyar fatan alheri ta yaki da cutar tarin fuka, da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS, ta yi kira ga ‘yan makarantar da su kasance masu yada kauna, su yada son juna tare da gudanar da rayuwa cikin farin ciki. Ta kuma yi kira gare su da su yi koyi daga abubuwan da suka gabata a shekaru 10 na tarihin makarantar.

Peng ta kara da cewa, cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, ta yi cudanya mai ma’ana da malamai da daliban wannan makaranta.

An dai gudanar da bikin ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ko “World AIDS Day” ta bana, bisa tsara wasu ayyuka masu nasaba da ranar a makarantar ta Linfen Red Ribbon, da ma bikin cikar makarantar shekaru 10 da kafuwa cikin nasara. (Saminu)