logo

HAUSA

Ana fatan kara inganta mu’amala da alaka tsakanin Sin da Afirka

2021-11-30 10:42:40 CRI

Ana fatan kara inganta mu’amala da alaka tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211130104032

Kwanan nan ne, sashin tuntubar kasashen waje na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ya kira wani muhimmin taro mai suna dandalin shugabannin matasan Sin da Afirka karo na biyar, inda kuma aka ilmantar da shugabanni gami da fitattun matasan Afirka kan muhimman batutuwan da aka tattauna kwanan baya a wajen cikakken zama na shida na kwamitin koli karo na 19 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Taron ya samu halartar wasu manyan shugabannnin kasashen Afirka, da na jam’iyyun siyasar su, gami da wasu wakilan matasa wadanda suka yi fice a Afirka.

Dandalin shugbannin matasan Sin da Afirka, wani muhimmin bangare ne a cikin dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Afirka. Kawo yanzu, an riga an yi irin wannan dandalin har sau hudu.

A nasa bangaren, shugaban sashin tuntubar kasashen waje na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Mista Song Tao ya gabatar da muhimmin jawabi, inda ya bayyana muhimman batutuwan da aka tattauna a wajen cikakken zama na shida na kwamitin koli karo na 19 na jam’iyyar kwaminis, gami da babbar ma’anar kudirin da aka zartas a gun taron, inda a cewarsa, bayan da aka gudanar da babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, gwamnatin kasar dake karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping tana bakin kokarinta wajen kyautata rayuwar al’umma, da taimakawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Mista Song ya jaddada cewa, jam’iyyar kwaminis ba raya al’ummun kasar Sin kawai take yi ba, har ma tana jajircewa wajen samar da alheri ga daukacin al’ummomin duniya. Mista Song ya ruwaito maganar shugaba Xi Jinping cewa, alakar Sin da Afirka ba a cikin rana daya ta ginu ba, ta inganta ne sakamakon matukar kokarin da bangarorin biyu suka yi mataki bisa mataki, inda ya ce:

“A karkashin tsarin dandalin FOCAC gami da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, kasar Sin da kasashen Afirka sun hada kai don tsarawa gami da aiwatar da wasu muhimman ayyukan hadin-gwiwa 10 da wasu manyan matakai 8. Tsawon layukan dogo da na hanyoyin mota da kasar Sin ta shimfida a Afirka dukka ya zarce kilomita 6000. Kuma kasar Sin tana taimakawa wajen aiwatar da wasu muhimman ayyukan samar da wutar lantarki da bada ilimi da aikin jinya a Afirka. Bayan bullar cutar COVID-19, kasar Sin da kasashen Afirka suna taimakawa juna, har ma Afirka ta fito fili don marawa kasar Sin baya wajen dakile yaduwar cutar, da kin amincewa da siyasantar da cutar. Ita kasar Sin ma tana samar da agajin aikin jinya da alluran riga-kafin cutar ga kasashen Afirka daban-daban, da tura kwararrun likitoci zuwa wurin, al’amarin da ya shaida irin dadadden zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu. Har ma shugaba Xi Jinping da takwarorinsa na kasashen Afirka sun hada kai don shirya taron yaki da annobar COVID-19, kuma sau da dama Xi ya jaddada muhimmancin samarwa Afirka isassun alluran riga-kafin bisa adalci.”

Mista Song ya jaddada cewa, matasa su ne makomar kowacce kasa, kuma muhimmin karfi wajen ingiza dangantakar Sin da Afirka. Ita jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dade tana maida hankali wajen inganta mu’amala da hadin-gwiwa tsakanin matasan Sin da Afirka. Mista Song yana fatan matasan bangarorin biyu za su kara bada tasu gudummawa wajen kyautata alakar kasar Sin da kasashen Afirka.

Daga cikin fitattun matasan Afirka da suka halarci dandalin bana, akwai wani mai suna Joseph Olivier Mendo’o, dalibi dan asalin kasar Kamaru wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a fannin dangantakar kasa da kasa a jami’ar Peking ta kasar Sin, kana shi ne shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin daliban Afirka a jami’ar, kana shugaban tawagar matasan Afirka dake kasar Sin.

Mista Mendo’o ya bayyana ra’ayinsa cewa, dandalin shugabannin matasan Sin da Afirka da aka shirya a wannan karo na da babbar ma’ana, ganin yadda matasa suke da kuzari da ilimi da hikimomi wajen raya kasashensu. A matsayin wani dan kasar waje wanda ya yi shekaru kusan shida yana karatu a Beijing, Mista Mendo’o yana maida hankali sosai kan sirrin ci gaban kasar Sin. A cewarsa, cikakken zama na shida na kwamitin koli karo na 19 na jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ya shaidawa duniya yadda kasar Sin ta samu manyan nasarori a baya, gami da hanyoyin da za ta bi wajen samun karin ci gaba.

Mista Mendo’o ya yi karin haske cewa:

“A ganina, babban dalilin da ya sa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta iya jagorantar al’ummun kasar don samun nasara shi ne, jagoranci nagari, kuma ta zabo wata hanyar da ta dace da yanayin ci gaban kasa, wato mai salon musamman irin na tsarin gurguzu. Kana, gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai a zahiri, musamman ganin yadda ta kan tsara shirye-shiryen raya kasa na gajeren lokaci, da na matsakaicin lokaci da kuma na dogon lokaci, don tsayawa haikan kan babban aikin samar da zaman jin dadi da alheri ga al’ummomin kasar. Saboda haka, a ganina matasan Sin da Afirka suna da buri da aiki iri daya, ya dace su yi koyi da juna don cimma burinsu tare.”

Shi ma a nasa bangaren, Mista Axel Jesson Ayenoue, mataimakin babban sakatare mai kula da harkokin matasa na jam’iyyar demokuradiyya mai mulkin kasar Gabon, wato Gabonese Democratic Party a turance, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa na yin koyi da dama daga wajen jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda ya ce:

“Na farko, mun yi koyi daga wajen jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wajen kafa sassan jam’iyyarrmu. Na biyu, mun koyi dabarun raya tattalin arziki daga wajen kasar Sin. Kamar yadda kasar Sin ta yi wajen kafa yankin musamman na raya tattalin arziki a birnin Shenzhen, kasar Gabon ita ma ta kafa irin wannan yanki don bunkasa sana’ar katako, har ma mun fara fitar da kayayyakin katako da muka sarrafa zuwa kasar Sin da sauran wasu kasashe abokan kasuwancinmu, abun da ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasarmu da samar da dimbin guraban ayyukan yi. Kasar Gabon ta yi irin wannan koyi ne daga kasar Sin a matsayin wani madubi, domin muna so mu koyi darussa daga nasarorin da kasar Sin ta samu.”

Raphael Tuju, shi ne sakatare janar na jam’iyyar Jubilee dake kasar Kenya, wanda ya zama daya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyun siyasar kasashen Afirka da suka halarci wannan dandali, inda ya gabatar da jawabin dake cewa:

“A halin da muke ciki a yau, kasar Sin ta kasance a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa mafi girma ga kasashen Afrika, kuma musamman a fannin ayyukan samar da ababen more rayuwa karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya,’ wanda shugaba Xi Jinping ya gabatar da ita. A matakin kasa da kasa kuwa, kasar Sin ta kasance a matsayin ginshiki wajen kokarin neman kyautata moriya da kokarin tabbatar da ci gaban kasashe masu tasowa. Jam’iyyar Jubilee tana mai bada tabbacin nuna goyon baya da tsayawa kan manufofin bai daya wadanda kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da su a cikin wadannan gwamman shekaru. Ya kamata mu mutunta manufofin kaucewa yin shisshigi a harkokin cikin gidan sauran kasashe. Muna goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, muna kan ra’ayi iri guda da kasar Sin na yin Allah wadai da duk wani yunkurin neman siyasantar da batun dokokin hakkin bil adama wanda ke neman yin mummunar illa ga moriyar kasashe wanda ya hada har da kasar Sin ba tare da martaba yanayin kasa da kuma salon da ya dace da kasar ba. Ina taya murna ga jam’iyyar CPC wacce ta bullo da wani salon tsarin shugabanci na demokaradiyya na zamani, abin koyi mai sigar musamman ta kasar Sin, lamarin da ya bayyana a fili cewa ba zai taba yiwuwa a fassara ma’anar demokaradiyya ko kare hakkin dan adam a tsari irin na bangare guda ba. Kuma babu wata kasa dake da ikon hawa kan mumbari ta gabatar da bayani ga sauran kasashe game da ma’anar mulkin demokaradiyya. Irin namijin kokarin da kasar Sin ta yi daga matakin kasa mai fama da talauci zuwa matsayin kasa mai karfin fada a ji a duniya, wato matsayin da take kai a yau ya kara kaimi ga kasashen dake da koma baya ta fuskar ci gaba. Ya dace mu kalli kasar Sin don samun kwarin gwiwa da kuma zama kyakkyawan abin koyi”. (Murtala Zhang)