logo

HAUSA

An bayyana dandalin FOCAC a matsayin ingantacciyar hanyar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika

2021-11-30 09:56:45 CRI

An bayyana dandalin FOCAC a matsayin ingantacciyar hanyar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika_fororder_211130-FOCAC-Faeza2

Wani sharhi da kafar yada labarai ta Amurka ta wallafa, ya bayyana dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, a matsayin wanda ya tabbatar da zama ingantaccen tsarin hadin gwiwar yankuna tsakanin Sin da Afrika.

Cikin wani sharhin, wanda aka wallafa a shafin intanet na kafar The Diplomat, marubucin wato Njumbe Smith, ya ce dandalin FOCAC ya zama daya daga cikin ingantattun tsarukan hadin gwiwa a karni na 21.

Njumbe Smith, dake karatun digiri na 3 a sashen huldar kasa da kasa da harkokin al’umma na jami’ar Fudan ta kasar Sin, ya ce, dandalin na zaman daya daga cikin dandamali na farko na hadin gwiwar kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa.

Ya ce yadda kasar Sin ta taimakawa kasashen Afrika wajen tunkarar annobar COVID-19, ya kara mata kaima a nahiyar, yana mai cewa, Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ta kasance mai cika alkawarin da ta dauka tun bayan kafuwarta, na samar da kayayyakin lafiya ga nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)