logo

HAUSA

Sin ta dinga kasancewa kasa mafi girma wajen cinikayya da kasashen Afirka cikin shekaru 12

2021-11-30 14:01:36 CRI

Sin ta dinga kasancewa kasa mafi girma wajen cinikayya da kasashen Afirka cikin shekaru 12_fororder_sin

Rahotannin da babban taron ‘yan kasuwa karo na bakwai, na dandalin taron tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ya fita jiya Litinin 29 ga wata, sun nuna cewa, kasar Sin ta dinga kasancewa kasa mafi girma a fannin gudanar da cinikayya da kasashen Afirka a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Alkaluman da aka samar sun kuma bayyana cewa, adadin jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya karu, daga dalar Amurka biliyan 2.17 a shekarar 2019 zuwa dala biliyan 2.96 a shekarar 2020, inda kasar Sin take zuba jari a kasashe 47 dake fadin nahiyar Afirka, musammam ma bayan da aka shirya dandalin FOCAC a shekarar 2000. Kasar Sin da kasashen Afirka sun gina sabuwar huldar abokantaka bisa tushen daidaito da moriyar juna. (Jamila)