logo

HAUSA

Sin na da yakinin hawa teburin shawara ne kadai zai kai ga warware batun nukiliyar Iran

2021-11-30 10:19:06 CRI

Sin na da yakinin hawa teburin shawara ne kadai zai kai ga warware batun nukiliyar Iran_fororder_211130-Iran-Saminu2

Wakilin Sin a ofishin MDD da sauran hukumomin kasa da kasa dake birnin Vienna Wang Qun, ya ce Sin na da yakinin cewa hawa teburin shawara ne kadai zai kai ga warware batun nukiliyar Iran. Don haka ya kamata Amurka ta dage dukkanin haramtattun takunkumai da ta kakabawa Iran da ma sauran wasu kasashe.

Wang Qun wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin da yake maraba da mataimakin ministan harkokin wajen Iran Ali Bagheri Kani, zuwa taron farko na tattaunawa da tawagar jami’an sabuwar gwamnatin Iran. Ya ce “An sake bude tattaunawa game da batun nan na nukiliya a Vienna, kuma muna fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan dama, su goyi bayan hanyar da aka dosa ta warware matsaloli bisa siyasa da diflomasiyya. Kaza lika su zamo masu kyakkyawan fatan cimma nasara tare da karbar sauyi, da martaba moriyar juna. Kaza lika su samar da kyakkyawan yanayi na warware rikici, da kawo karshen sabani da ake fuskanta ta hanyar tattaunawa.

Wang Qun ya kara da cewa, a matsayinta na wadda ta sabbaba takaddamar nukiliyar Iran da ake fama da ita a yanzu, kamata ya yi Amurka ta dage dukkanin haramtattun takunkumai da ta kakabawa Iran din, da ma sauran wasu kasashe ciki har da Sin, domin kaiwa ga sake samun amincewar sassan kasa da kasa. A hannu guda kuma, ya kamata ita ma Iran ta cika dukkanin sharuddan ta a wannan fanni.

Wang ya ce Sin za ta ci gaba da kare ’yancin ta halas, da moriyar ta a fannin kawar da takunkumai da aka kakaba mata, da ma a sauran bangarori.  (Saminu Alhassan)