logo

HAUSA

WHO: Ba a kai ga tantance ko nau’in Omicron ya fi saurin yaduwa da illa ga bil adama ba

2021-11-29 09:45:51 CRI

WHO: Ba a kai ga tantance ko nau’in Omicron ya fi saurin yaduwa da illa ga bil adama ba_fororder_1129-Saminu1-WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kawo yanzu, ba a kai ga tantance ko nau’in Omicron na cutar COVID-19 ya fi saurin yaduwa da illa ga lafiyar bil adama ba. Kaza lika babu tabbas game da tasirin nau’in cutar sama da sauran nau’o’in kamar na Delta.

WHO wadda ta bayyana hakan a jiya Lahadi, ta ce zai dauki lokaci kafin tantance yanayin tasirin wannan nau’i na cutar COVID-19, duk da cewa adadin masu harbuwa da ita na karuwa, ana kuma kwantar da masu kamuwa da ita a Afirka ta kudu.

A daya bangaren kuma, WHO ta ce ba a kai ga tabbatar da ko nau’in na Omicron na haifar da wasu alamun ciwo na daban sabanin na sauran nau’o’in cutar COVID-19 ba, saboda gane hakan kan dauki kwanaki ko ma makwanni.

WHO ta tabbatar da cewa, dukkanin nau’o’in COVID-19, ciki har da nau’in Delta wanda shi ne mafi yaduwa a duniya na iya haifar da ciwo mai tsanani ko asarar rayuka, musamman ga rukunin mutane masu raunin, don haka daukar matakan kandagarki shi ne mafi tasiri.  (Saminu)