logo

HAUSA

Xi Jinping: Kasar Sin Za Ta Hada Kai Da Kasashen Afirka Wajen Gudanar Da Ayyuka 9 Tare

2021-11-29 21:28:49 CRI

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing na kasar Sin, tare da ba da jawabi.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta samar wa kasashen Afirka karin alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 1, a kokarin tabbatar da manufar kungiyar Tarayyar Afirka wato AU na yi wa al’ummomin Afirka da yawansu ya kai kaso 60 cikin dari allurar a shekarar 2022. A cikin wadannan allura, miliyan 600 daga cikinsu kasar Sin za ta samar da su ne kyauta, miliyan 400 kuma kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka masu ruwa da tsaki ne za su samar da su.

Shugaban kasar Sin ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta taimaka wa kasashen Afirka wajen aiwatar da shirye-shirye guda 10 na rage talauci da aikin gona, za ta kuma tura kwararru a fannin aikin gona 500 zuwa kasashen Afirka, tare da kafa wasu cibiyoyin zamani da gwaji da ba da horo ta fuskar fasahar aikin gona tsakanin Sin da Afirka a kasar Sin. Ban da haka kuma, kasar Sin za ta karfafawa hukumomi da kamfanoninta gwiwa da su kafa yankunan gwaji ta fuskar raya aikin gona da rage talauci a kasashen Afirka.

Har ila yau Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin za ta hada kai da kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan guda 9, ta fuskar kiwon lafiya, rage talauci da ba da gatanci ga manoma, kara azama kan ciniki, zuba jari, yin kirkire-kirkire ta fuskar fasahar zamani, raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, kyautata kwarewar mulki, yin mu’amalar al’adu da tsaron kasa da shimfida zaman lafiya.

Shugaban kasar Sin ya yi bayani da cewa, ya yi imani cewa, sakamakon kokarin da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi tare, ya sa tabbas taron zai samu cikakkiyar nasara, zai kuma hada karfin al’ummomin Sin da Afirka da yawansu ya kai biliyan 2.7 baki daya wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka baki daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan