logo

HAUSA

Rahoto: Manufar Amurka na raba kawuna da nuna adawa da dunkulewar duniya ya haifar da tsadar farashi a Amurkar

2021-11-29 10:24:08 CRI

Rahoto: Manufar Amurka na raba kawuna da nuna adawa da dunkulewar duniya ya haifar da tsadar farashi a Amurkar_fororder_1129-Ahmad2-Farashin Kaya na Amurka

Wani rahoto da kafar yada labarai ta Singapore ta fitar ya bayyana cewa, manufofin Washington na haifar da baraka tsakaninta da kasar Sin, da nuna adawa da dunkulewar duniya, da kuma yadda take tinkarar batun sauyin yanayi sun kasance a matsayin manyan dalilan dake haddasa karuwar tashin farashi a kasar Amurkar tun bayan barkewar takaddamar kasuwanci tsakaninta da kasar Sin da kuma bullar annobar COVID-19.

A sharhin da jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta wallafa a ranar Juma’a ta bayyana cewa, alkaluman tashin farashin kayan masarufi a Amurka ya karu da kashi 6.2 bisa 100 a watan Oktoba idan an kwatanta da shekarar bara, kasar na fuskantar tashin farashin kayayyaki cikin sauri da ba ta taba ganin irinsa ba tun a shekarar 1990.

A cewar sharhin, tsarin karbar rancen kudade da kasuwannin hada hadar kudi na kasar su ma na daga cikin dalilan dake kara ta’azzara tashin farashin kayayyakin a kasar. (Ahmad Fagam)