logo

HAUSA

Rahoto: Amurkawa ne ke biyan tasirin harajin da tsohuwar gwamnatin Trump ta kakabawa hajojin Sin

2021-11-29 09:51:59 CRI

Rahoto: Amurkawa ne ke biyan tasirin harajin da tsohuwar gwamnatin Trump ta kakabawa hajojin Sin_fororder_1129-Saminu2-Cinikin Sin da Amurka

Jaridar “The New York Times” ta Amurka, ta bayyana cewa, Amurkawa ne ke biyan nauyin harajin da tsohuwar gwamnatin shugaba Trump ta kakabawa hajojin Sin.

Cikin wani rahoto da ta wallafa a baya bayan nan, jaridar ta ce maimakon aiwatar da manufofin zuwa jari masu dogon zango, wadanda za su taimakawa kamfanonin Amurka farfadowa, gwamnatin kasar mai ci ta himmatu wajen dakile takara, matakin da ke kunshe da gazawa, wanda kuma ke da tsadar aiwatarwa, da kuma mummunan sakamako.

Rahoton ya kara da cewa, makasudin dora haraji kan hajojin Sin shi ne hukunta kamfanonin ta, amma kuma daga karshe Amurkawa ne ke biyan nauyin harajin daga aljihunsu.

Daga nan sai rahoton ya yi kira ga gwamnatin shugaba Joe Biden, da ta yi watsi da munanan manufofin tsohuwar gwamnatin Trump, ta kuma dakatar da damuwar da take nunawa game da kasar Sin.  (Saminu)