logo

HAUSA

Najeriya ta janye dakatarwar da ta yiwa kamfanin jiragen saman Emirates

2021-11-28 16:13:56 CRI

Gwamnatin Najeriya ta janye dakatarwar da ta yiwa kamfanin jiragen saman Emirates na hadaddiyar daular Larabawa UAE, daga sauka ko tashi a kasar ta yammacin Afrika ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

Matakin hakan ya zo ne sakamakon bukatar da ‘yan Najeriya masu yin tafiye-tafiye suka nuna, kana bayan yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin jiragen na UAE da ya kafa babban zaurensa a Dubai, kamar yadda ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ya bayyana a wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A watan Maris na shekarar bana gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jirgin saman na Emirates daga sauka ko a tashi a Najeriyar saboda UAE ta nuna bambanci ga ‘yan Najeriya dangane da wasu ka’idojin yaki da annobar COVID-19.

A cewar wasu rahotannin kafafen yada labarai, UAE ta tilastawa fasinjoji ‘yan Najeriya yin karin wasu gwaje-gwaje wadanda sun ci karo da ka’idojin da Najeriya ta tsara game da gwajin cutar a filayen jiragen sama na Lagos da Abuja gabanin tashi daga filayen jiragen saman.

Sirika ya ce, UAE ta janye wasu ka’idojin da ta sanyawa ‘yan Najeriyar. Ya kara da cewa, sun samu bayanai daga hadaddiyar daular Larabawa na janye wasu ka’idojin dake tada hankalin matafiya. Don haka, sun yanke shawarar janye haramcin da suka yiwa jiragen saman na  Emirates.(Ahmad)

Ahmad