logo

HAUSA

Tsokaci Kan Huldar Kasuwanci Da Tattalin Arziki Tsakanin Sin Da Afrika

2021-11-28 17:15:54 CRI

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda takardar bayanai a ranar Juma’a, inda ya yi cikakken bayani game da hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika a sabon zamanin da muke ciki.

Bayanan sun nuna cewa, hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Afrika ta yi matukar bunkasa cikin sauri kuma ta kai matsayin koli a kusan shekaru 10, lamarin da ya kara azama kan ci gaban nahiyar Afirka da kuma haifar da babbar moriya ga al’ummun bangarorin biyu.

Wadannan hujjoji da alkaluma da za a gabatar sun kara bayyana hakikanin nasarori da aka cimma karkashin huldar ciniki da tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu.

Kasar Sin ta dauki shekaru 12 a jere ta zama ta farko a duniya wajen yin kasuwanci da kasashen Afirka tun daga shekarar 2009. Alkaluman kasuwancin da Afrika ta gudanar tsakaninta da Sin bisa yawan jimillar cinikayyar da nahiyar ta gudanar a duniya suna ci gaba da karuwa, inda karuwar ta zarce kashi 21 bisa 100 a shekarar 2020.

Kasar Sin ta kara yawan kayayyakin dake shigo da su daga kasashen Afrika, kana ta soke harajin da take karba kan kayayyakin da yawansu ya kai kaso 97 cikin dari daga dukkan kayayyakin da take shigowa daga kasashe 33 mafiya koma bayan tattalin arziki a Afrika.

Adadin cinikayyar hidima da kasar Sin ke shigowa daga Afrika yana ci gaba da karuwa da kusan kashi 20 bisa 100 a duk shekara tun daga shekarar 2017, lamarin dake taimakawa wajen samar da guraben ayyukan yi kusan 400,000 a nahiyar a duk shekara.

Ya zuwa karshen shekarar 2020, jarin kai tsaye da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Afrika ya zarce na dalar Amurka biliyan 43.

Kasar Sin ta kafa kamfanoni sama da 3,500 nau’ika daban daban a dukkan fadin nahiyar Afirka, inda sannu a hankali kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin suke kara zama wani ginshi a fannin zuba jari a Afrika. Sama da kashi 80 bisa 100 na ma’aikatan kwadago da suke aiki a kamfanonin ‘yan cikin gidan kasashen ne, haka kuma an samar da miliyoyin guraben ayyukan yi na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba a Afirka.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kafa tsarin hadin gwiwa a fannin aikin gona da kasashen Afrika da kuma kungiyoyin shiyyar guda 23, kana ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin yin hadin gwiwar aikin gona guda 72 tsakanin bangarori 2 da bangarori da dama.

Ya zuwa karshen shekarar 2020, sama da kamfanonin kasar Sin 200 sun zuba jarin dalar Amurka biliyan 1.11 a fannonin shuke-shuke, renon dabbobi, aikin sarrafawa da dai sauransu a kasashen Afrika 35.

Ya zuwa karshen watan Oktoban 2021, tsarin biyan kudi tsakanin bankuna a tsakanin kasa da kasa ya samu abokan hulda na kai tsaye 42 a kasashen Afrika 19. Bankin jama’ar kasar Sin ya sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudade da manyan bankuna na kasashen Afrika ta Kudu, Morocco, Masar, da Najeriya, wanda ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 73 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 11.(Ahmad)

Ahmad