logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da Afirka na shekarar 2021

2021-11-28 17:29:30 CRI

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da Afirka na shekarar 2021_fororder_1128-3

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasar Sin da kasashen Afirka na shekarar 2021 wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya karbi bakuncin gudanar da shi a ranar 26 ga wannan wata a birnin Nairobi dake kasar Kenya, mahalartar taron kimanin 100 daga Sin da kasashen Afirka 43 sun yi taron ta kafar bidiyo.

Memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin fadakar da jama’a na kasar Sin Huang Kunming ya yi jawabi ta kafar bidiyo inda ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, kafofin watsa labaru na kasar Sin da na kasashen Afirka sun watsa labaru bisa tushe cikin adalci, da nuna sahihanci da juna da sa kaimi ga sada zumunta a tsakanin jama’a, da kiyaye yin kirkire-kirkire, da raya fasahohin sadarwa, ta hakan an gwada labarai da dama dake shaida zumunta a tsakanin Sin da Afirka. A nan gaba, za a ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin kafofin watsa labaru, da masana, da al’adu da sauransu don yin kokarin raya duniya mai kyau tare da kasashen Afirka.

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da Afirka na shekarar 2021_fororder_1128-4

A wajen taron, an kafa kawancen abokan Afirka. Kana cibiyar watsa labaru ta Asiya da Afirka ta CMG da kafofin watsa labaru na kasar Nijeriya sun kaddamar da shirin hadin gwiwar kafofin watsa labaru masu amfani da harshen Hausa. Cibiyar fassara wasan kwaikwayo ta CMG da kasashen Afirka 5 sun daddale yarjejeniyar gabatar da wasan kwaikwaiyo na kasar Sin, tare da yin bayani game da yanayin gabatar da wasan kwaikwayo da shirye-shiryen Sin ga kasashen Afirka wato The Bond karo na biyu, da kuma gasar kacici-kacici game da wannan biki. A cikin wata guda, an gabatar da wasan kwaikwayo da shirye-shiryen Sin fiye da 50 masu amfani da harsuna shida a kafofin watsa labaru na kasashen Afirka 20, wadanda suka jawo hankalin masu kallo kimanin miliyan 300, da mutane fiye da miliyan 140 suka tattauna kan su a internet, kuma an samu wasiku dubu 26 daga masu kallo daga kasashen duniya 86. (Zainab)