logo

HAUSA

Tsohon Shugaban Najeriya: Inganta Kyakkyawar Dangantaka Da Kasar Sin Zai Tabbatar Da Moriyar Juna

2021-11-28 20:53:57 CRI

Tsohon Shugaban Najeriya: Inganta Kyakkyawar Dangantaka Da Kasar Sin Zai Tabbatar Da Moriyar Juna_fororder_najeriya

Shugaban majalisar tattaunawa ta tsoffin shugabannin kasashen duniya wato InterAction Council, kana tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana a yayin tattaunawa da wakilin gidan talabijin na CGTN, Deji Badmus cewa, yana fatan taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC karo na takwas zai tattauna abubuwan da Afrika ke bukata a yayin da ta samu taimakon kasar Sin, domin nahiyar ta samu damar tsayawa da kafafunta, wajen inganta fannin kiwon lafiya don dakile annobar COVID-19. Ya kara da cewa, inganta kyakkyawar huldar dake tsakanin Sin da Afrika zai samar da moriya ga dukka bangarorin biyu.(Ahmad)

Ahmad