logo

HAUSA

Nahiyar Afrika ba dandalin gasa ne tsakanin manyan kasashe ba

2021-11-27 21:26:53 CRI

Nahiyar Afrika ba dandalin gasa ne tsakanin manyan kasashe ba_fororder_54fbb2fb43166d229b28ce89bceb75fe9152d2a7

Mai taimakawa ministan harkokin wajen Sin, Wu Jianghao, Ya ce bai kamata nahiyar Afrika ta zama dandalin gasa tsakanin manyan kasashe ba, sai dai dandalin hadin gwiwar kasa da kasa.

Wu Jianghao ya bayyana yayin wani taron manema labarai da aka yi jiya a birnin Beijing cewa, taimakawa nahiyar Afrika, hakki ne na bai daya, da ya rataya a wuyan kasa da kasa.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da fatan ganin hadin gwiwar sauran kasashe da na nahiyar Afrika.

Da yake jaddada wannan batun, shugaban sashen kula da harkokin nahiyar Afrika na ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wu Peng, ya ce ya zama wajibi bukatun Afrika ya kasance jigo cikin hadin gwiwar Sin da Afrika da hadin gwiwar sauran kasashe da Afrika. (Fa’iza Mustapha)