logo

HAUSA

Israela ta haramtawa kasashen Afrika 7 shiga kasarta sakamakon sabon nau’in cutar COVID-19

2021-11-26 11:03:45 CMG

Israela ta haramtawa kasashen Afrika 7 shiga kasarta sakamakon sabon nau’in cutar COVID-19_fororder_211126-A2 Isra'ila

Kasar Israela ta sanar a ranar Alhamis cewa, ta haramtawa fasinjoji daga wasu kasashen Afrika bakwai shiga kasarta, sakamakon bullar sabon nau’in cutar COVID-19 a kasar Afrika ta Kudu.

A yayin da ake samun rahotannin barkewar sabon nau’in cutar mai suna B.1.1529, firaministan Israela Naftali Bennett, da ministan lafiyar kasar Nitzan Horwitz, sun yanke shawarar sanya kasashen Afrika ta kudu, da Lesotho, da Botswana, da Zimbabwe, da Mozambique, da Namibia da kuma Eswatini a matsayin kasashe mafiya hadari, kamar yadda sanarwar da ofishin firaministan kasar ta bayyana cewa mutanen da suka fito daga wadanan kasashen, ba zasu samu damar shigar Isra’ila ba.(Ahmad)

Ahmad