logo

HAUSA

WHO: Kimanin kashi 27 na ma'aikatan kiwon lafiya a Afirka sun karbi cikakkiyar allurar rigakafin COVID-19

2021-11-26 14:50:18 CMG

WHO: Kimanin kashi 27 na ma'aikatan kiwon lafiya a Afirka sun karbi cikakkiyar allurar rigakafin COVID-19_fororder_12

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, kashi 27 cikin 100 na ma'aikatan kiwon lafiya a Afirka ne kawai aka yi wa allurar rigakafin cutar COVID-19, lamarin da ya sa akasarin ma'aikatan da ke sahun gaba wajen yakar cutar ba su da kariya.

Ofishin WHO dake yankin Afirka ya bayyana cewa, ana fama da karancin ma'aikatan kiwon lafiya a Afirka, yayin da kasashe 16 dake yankin ke da kasa da ma'aikatan kiwon lafiya guda daya a cikin 1,000.

Ya zuwa yanzu, an yi alluran rigakafi sama da miliyan 227 a Afirka. Kana kasashe 39 da suka ba da bayanai game da riga kafin na nuna cewa, kimanin alluran riga kafi miliyan 3.9 ne, aka yiwa ma'aikatan kiwon lafiya.

A cewar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuta ta Afira, ya zuwa yammacin ranar Alhamis, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, ya kai 8,614,525, mutane 222,254 kuma suka mutu, yayin da 8,060,459 suka warke daga cutar.(Ibrahim)

Ibrahim