logo

HAUSA

Iran ta ce akwai yiwuwar kulla yarjejeniya da hukumar IAEA

2021-11-25 11:20:28 CRI

Iran ta ce akwai yiwuwar kulla yarjejeniya da hukumar IAEA_fororder_211125-ahmad-2-Iran

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian, ya wallafa a shafinsa na twita cewa, mai yiwuwa ne a cigaba da yarjejeniya da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA), kuma a nan gaba kadan za a gudanar da tattaunawa kan batun.

Amir Abdollahian ya bayyana cewa, muhimmiyar tattaunawa, ta gaskiya, kuma mai alfanu, da suka gudanar tare da babban daraktan hukumar IAEA Rafael Grossi, a Tehran a ranar Talata, sun cimma kyakkyawar matsaya na ci gaba da gudanar da hadin gwiwa.

Ministan harkokin wajen na Iran ya yi wannan tsokaci ne domin mayar da martani kan tsokacin da Grossi ya yi game da ziyararsa zuwa Tehran da yake nuna cewa har yanzu ba ta kammala ba, kamar yadda ya bayyana a lokacin taron hukumar daraktocin da aka saba gudanarwa bayan watanni uku wanda ya gudana a birnin Vienna. (Ahmad)