logo

HAUSA

Sin: Duk wanda ke neman siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya, zai haifarwa kansa da illa

2021-11-24 21:19:35 CRI

Kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Rasha ya ce, kasar Amurka da wasu kasashen Turai suna matsawa kasashen duniya lamba, don su daina yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kasar Rasha da ma kasar Sin. Amma, kasar Rasha ba ta taba yin haka ba, kasar Rasha ta na girmama ikon kasashen duniya na zaben abokan hadin gwiwa.

Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Laraba cewa, wasu kasashe da kawayen su, suna neman siyasantar da harkokin tattalin arziki da cinikayya, matakin da zai bata tsarin cinikin kasa da kasa, ya kuma haddasa barazana ga tsarin samar da kayayyaki tsakanin kasa da kasa, lamarin da zai haifar da matsala ga kasashen duniya, da ma su kansu. (Maryam)