logo

HAUSA

Marubucin Ba’Amurka ya yi gargadi kan hadarin dake tattare da samun baraka tsakanin Amurka da Sin ga tattalin arzikin duniya

2021-11-24 11:35:18 CRI

Marubucin Ba’Amurka ya yi gargadi kan hadarin dake tattare da samun baraka tsakanin Amurka da Sin ga tattalin arzikin duniya_fororder_1124-tattalin  arzikin Sin da Amurka-Ahmad

Wani mai sharhi na kasar Amurka a kwanan nan ya yi gargadi game da mummunan tasirin rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen Amurka da Sin wato kasashe mafi karfin tattalin arziki, wadanda ke samar da sama da kashi 40 bisa 100 na jimillar arzikin duniya.

Daniel DePetris, mai sharhi a sashen al’amurran kasashen waje na mujallar Newsweek ta Amurka wacce ake wallafa ta mako-mako, ya bayyana cewa, samun cikakkiyar baraka tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya babu abin da zai haifar wa kasa da kasa face koma baya, kuma sakamakon hakan zai iya haifar da rashin tabbas a kasuwannin hada hadar kudade ta duniya.

DePetris ya jaddada cewa, babu wani batu da za a iya bayyanawa a matsayin “wani bangare guda shi ne ya fi cancanta sama da dukkan manufofin kasar Sin."

Ya kara da cewa, tilas ne Amurka ta bullo da wani tsari wanda zai dauki alhakin dukkan wadannan mabambantan batutuwa, ko ma wane irin mataki ne kasar Sin ta dauka na yin mahawara a cikin gida. (Ahmad)