logo

HAUSA

Jami’ar MDD ta yi kira da a sabunta matakan yaki da safarar mutane a duniya

2021-11-23 09:55:20 CRI

Jami’ar MDD ta yi kira da a sabunta matakan yaki da safarar mutane a duniya_fororder_211123-yaya-3

Mataimakiyar babban sakatare janar na MDD Amina Mohammed, a jiya Litinin, ta yi kira da a sabunta matakan yaki da safarar mutane a duniya.

Jami’ar ta yi wannan kiran ne, yayin taron manyan jami’ai na babban taron MDD kan kimanta shirin MDD na kimanta yaki na fataucin mutane. Tana mai cewa, akwai bukatar sabuntawa da kuma karfafa matakan kasashen duniya game da wannan laifi na fataucin bil-adama fiye da kowane lokaci, a gabar da matsalolin tattalin arziki, da rikice-rikice, da matsalolin lafiya da yanayi ke karuwa, da ma kara rauni ga fataucin, da kuma cin zarafi

Ta ce, hadin gwiwar kasa da kasa na da managartan kayan aiki na hanawa da kawo ƙarshen fataucin mutane. Sai dai kuma, matakan magance wannan matsala a zahiri suna ci gaba da bambanta matuka. A don haka, akwai bukatar samar da karin taimako na fasaha da tallafi don karfafa matakai na bai daya. Ta kara da cewa, akwai bukatar mambobin kasashe su inganta hadin gwiwa a fannin musayar bayanai, da ayyukan shari'a da sauransu. Haka kuma, akwai bukatar a kara kaimi, domin kare bakin haure masu rauni daga fadawa tarkon masu fataucin mutane. (Ibrahim)