logo

HAUSA

Dandalin al’ummun Sin da Afirka yana taimakawa wajen kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka

2021-11-23 14:40:13 CRI

Dandalin al’ummun Sin da Afirka yana taimakawa wajen kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211121185404

Kwanan nan ne, aka gudanar da dandalin al’ummun kasar Sin da kasashen Afirka karo na shida a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wato China Africa People’s Forum a turance, inda jami’an gwamnatoci da shugabannin jam’iyyun siyasar kasashen Afirka sama da 30, da jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, gami da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Sin suka halarci taron.

Shirya dandalin al’ummun Sin da Afirka, na daya daga cikin muhimman ayyuka na tsarin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wanda aka fi sani da FOCAC a takaice, da zummar sada zumunta, da fadada hadin-gwiwa da shimfida zaman lafiya a duk fadin duniya. Tun daga shekarar 2011 ya zuwa yanzu, an riga an gudanar da irin wannan dandali har sau biyar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon murnar shirya taron na bana, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu duniya na fuskantar babban ci gaba da manyan sauye-sauye, ya dace kasar Sin da kasashen Afirka su tsaya haikan wajen wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, da shimfida adalci da bin tafarkin demokuradiyya da neman ‘yanci, a kokarin tinkarar sabbin kalubaloli. Shugaba Xi yana kuma fatan Sin da Afirka za su kara raya dandalin al’ummun Sin da Afirka, don ya zama tamkar muhimmiyar gada ta samun fahimtar juna tsakanin su, da zama tamkar abin koyi ga raya al’ummun Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, ta yadda za’a bude sabon babi ga sada zumunta a tsakaninsu.

Dandalin al’ummun Sin da Afirka yana taimakawa wajen kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211121185410

Mataimakin shugaban majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, kana shugaban kungiyar mu’amala da kasashen waje ta kasar Sin, Mista Ji Bingxuan ya gabatar da jawabi a wajen taron dandalin, inda ya ce, sakon shugaba Xi Jinping ya bayyana yadda jam’iyyar kwaminis gami da gwamnatin kasar Sin suke matukar maida hankali kan raya dangantakar abokantaka tare da kasashen Afirka, da karfafa mu’amala da hadin-gwiwa a tsakanin al’ummun kasar Sin da na Afirka. Haka kuma sakon Xi ya kafa alkibla ga ci gaba da yayata zumuncin gargajiya da samar da alherai ga al’ummun bangarorin biyu.

Mista Ji Bingxuan ya bayyana cewa:

“Bayan barkewar cutar mashako ta COVID-19, Sin da Afirka sun zama tamkar tsintsiya madaurinki daya wajen tinkarar annobar, da shawo kan kalubaloli da dama, da ci gaba da raya ayyukan shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, da kin amincewa da siyasantar da batun, ko kuma nuna kabilanci da bambancin ra’ayi kan mabambantan tsarin siyasa. Zumuntar dake tsakanin Sin da Afirka na dada inganta cikin dogon lokaci, kuma na kara samun makoma mai haske.“

Mista Ji ya ci gaba da cewa, bana ake cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin. Kuma tun daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Nuwambar bana, an kira cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiya karo na 19 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Beijing, inda aka ayyana manyan nasarorin da jam’iyyar JKS ta samu gami da darussan da ta koya cikin shekaru 100. Jam’iyyar JKS ta dade tana kokarin tabbatar da shimfida tsarin demokuradiyya a duk fadin kasar Sin, kana ta yi kira a shimfida tsarin demokuradiyyar a bisa dangantakar kasa da kasa, wato duk wata kasa, ko babba, ko karama, dole ne a mutunta juna.

Mista Ji ya ce:

“Tun kafuwar dandalin al’ummun Sin da Afirka har zuwa yanzu, dandalin yana maida hankali wajen sada zumunta da karfafa hadin-gwiwa tsakanin al’ummomun kasar Sin da kasashen Afirka, wanda ya taka muhimmiyar rawa a fannin samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu. Ginawa gami da ci gaba da raya dandalin al’ummun Sin da Afirka, ya tabbatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya. Hausawa kan ce, hannu daya ba ya daukar jinka. Ina fatan za mu yi kokari tare don aza tubali mai inganci ga raya al’ummun Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da tattaro hikimomin al’umma wajen raya kyakkyawar dangantakar Sin da Afirka.”

Dandalin al’ummun Sin da Afirka yana taimakawa wajen kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211121185415

Shi ma a nasa jawabin, jakadan kasar Tanzaniya dake kasar Sin Mista Mbelwa Kairuki ya ce, taken taron na wannan karo, ya dace da yanayin da duniya ke ciki game da fama da barkewar annobar COVID-19 da kuma matsalar karayar tattalin arziki, inda ya ce:

“Wannan annoba, ta kara tunatar da mu cewa duniya muna rayuwa ne a bisa ruhi guda kuma idan ba mu hada kai ba za mu iya wayar gari cikin yanayi na kara tabarbarewar al’amura, sannan kuma tana kara nuna mana cewa, za mu iya samun makomar bai daya ne kadai ta hanyar daukar matakan magance matsaloli na bai daya hakan shi ne zai taimaka mana wajen samun al’umma mai makomar bai daya. A wannan halin da muke ciki, akwai matukar muhimmanci mu hada hannu wuri guda da yin aiki tare da junanmu domin dakile illolin annobar kuma mu kara ci gaban da aiwatar da manufofinmu. Ina da kyakkyawan kwarin gwiwa cewa sakamakon da aka samu a taron dandalin hadin gwiwar al’ummun Sin da Afrika da aka gudanar a wannan karo, a karshen wannan dandali zai kara yin tasiri a taron ministocin mambobin kungiyar hadin gwiwar Sin da Afrika karo na takwas wanda ake sa ran gudanarwa cikin wannan wata a kasar Senegal dake nahiyar Afrika. Taron ministocin yana da alfanu kuma zai samu kyakkyawan karbuwa ga kasashen Afrika da kuma kasar Sin matukar ya mayar da hankali kan batutuwan dake shafar al’ummun kasashen. Ina fadar hakan ne saboda burin da ake da shi na cimma nasarar kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya zai amfanawa al’ummarmu kuma za su tabbatar da dorewarsa. Za mu iya cimma wannan buri ne ta hanyar mayar da hankali wajen biyan muradun al’umma, da cika musu burikansu, da warware matsalolin dake shafar al’ummar, da magance kalubalolinsu, kuma tabbas babu wani waje mafi dacewa na gabatar da irin wadannan shawarwari sama da wannan dandali wanda ya kasance daga mutane, dake shafar mutane, kuma don amfanin mutane.”

Bugu da kari, jakadan Tanzaniya dake kasar Sin Mista Mbelwa Kairuki ya yi amfani da wannan dandali wajen kara yin kira ga al’ummun kasashen Afrika da na Sin, su yi kokari wajen renon hadin gwiwar Sin da Afrika wacce ta shafe shekaru fiye da 60. Haka zalika, ba za’a taba mantawa da irin rawar da al’ummu maza da mata na kasashen Afrika da Sin suka taka ba wajen tabbatar dinkewar alakar dake tsakanin bangarorin biyu. Ba za’a taba mancewa da irin gudunmawar da tawagar kwararrun likitocin kasar Sin suka yi wajen sadaukar da rayuwarsu suka bar gidajensu zuwa Afrika don taimakawa tsarin lafiyar al’ummar Afrika ba. Ba za’a taba mantawa ba a watan Satumbar 2014, a lokacin da likitoci daga kasar Sin suka je kasar Saliyo inda suka yi aiki tare da takwarorinsu na kasar Saliyo domin dakile annobar Ebola kuma ba za’a taba mantawa ba. Haka zalika a watan Mayun 2020, a lokacin da tawagar jami’an lafiya daga yankin Chongqing suka isa kasashen Laberiya da Sudan domin bayar da tallafi irin na kwararru ga likitoci dake kasashen domin kawar da annobar COVID-19.

Dandalin al’ummun Sin da Afirka yana taimakawa wajen kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20211121185421

A nata bangaren, mataimakiyar shugabar kungiyar hadin-gwiwar matan kasar Sin, Madam Huang Xiaowei ta gabatar da jawabi, inda ta gabatar da dimbin nasarorin da matan kasar suka samu musamman a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, da kuma yadda ake yin cudanya da mu’amala tsakanin matan kasar Sin da takwarorinsu na kasashen Afirka da dama.

Madam Huang ta bayyana cewa:

“Bana ake cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. A cikin shekaru 100, jam’iyyar JKS tana maida hankali sosai wajen tabbatar da daidaiton jinsi da samar da ci gaba ga harkokin mata. A karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, harkokin matan kasar Sin sun samu manyan nasarori da ba’a taba ganin irinsu ba a tarihi, har ma an tsara buri na musamman don samar da ci gaba ga mata. A cikin mutane miliyan 98.99 da gwamnatin kasar Sin ta fito da su daga kangin talauci, mata sun dauki kusan rabi. Matan kasar Sin suna kara jin dadin rayuwa da aiki a halin yanzu.”

Madam Huang ta kara da cewa, duk da cewa akwai nisan gaske tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka, amma matanensu na da buri irin daya, wato neman samun daidaiton jinsi da ci gaba. Matan kasar Sin na son kara yin mu’amala da zurfafa hadin-gwiwa da matan Afirka, da tabbatar da daidaiton jinsi da baiwa mata hakkoki yadda ya kamata, domin bayar da sabuwar gudummawa wajen raya al’ummun Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)