logo

HAUSA

Sin da Rasha sun kira taron karawa juna sani kan hakkin bil adama a Geneva

2021-11-20 16:31:13 CRI

Sin da Rasha sun kira taron karawa juna sani kan hakkin bil adama a Geneva_fororder_taro

Ofisoshin din din din na Sin da Rasha dake ofishin MDD dake Geneva, sun kira wani taron karawa juna sani ta kafar intanet, mai taken: “demokradiyya da hakkokin dan adam: buri na bai daya, kyakkyawar al’ada”.

Wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, ba tare da la’akari da irin tsarin da kasa ta runguma ba, jama’a su ne jagororinta, abun dake nufin demokardiyya ta ainihi. Ya ce a lokacin da jama’a suka kasance mafi muhimmanci ne kadai za a cimma kare hakkokinsu. Ya kara da cewa, tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe bisa fakewa da demokradiyya da hakkon bil adama, da kuma takala, rikici da tashin hankali kadai za su haifar.(Fa’iza Mustapha)