logo

HAUSA

Shawarar ziri daya da hanya daya na kyautata rayuwar karin jama’a

2021-11-20 19:57:41 CRI

Shawarar ziri daya da hanya daya na kyautata rayuwar karin jama’a_fororder_ziri daya

Yayin taro karo na 3, kan shawarar ziri daya da hanya daya da aka yi jiya a Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada ingantattun burikan ci gaba na shawarar, yana mai cewa, amfanawa rayuwar jama’a, daya ne daga cikinsu.

Cikin shekaru 8 da suka gabata, shawarar ziri daya da hanya daya ta samu tagomashi, inda ta yi fice a duniya. Ta kuma zama madubi ga kasar Sin wajen fadada bude kofarta da inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.

A cewar rahoton nazari na bankin duniya, zuwa shekarar 2030, ana sa ran shawarar ziri daya da hanya daya za ta taimaka wajen fitar da mutane miliyan 7.6 daga matsanancin talauci, yayin da za ta fitar da wasu miliyan 32 daga matsakaicin talauci. (Fa’iza Mustapha)